Hukumar NSCDC ta bayyana shirin ba da tsaro dangane da zabe a Gombe
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta NSCDC a Jihar Gombe ta ce ta shirya tsaf don tunkarar zabubbukan bana da za a fara a gobe Asabar. Kwamandar Hukumar ta Jihar, Hajiya Altine Sani Umar ce ta bayyana haka a shekaranjiya Laraba lokacin da take ganawa da manyan jami’an hukumar don isar da sakon Babban Kwamandansu […]
Kwamandar Hukumar Civil Defence ta Jihar Gombe Hajiya Altine Sani Umar
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta NSCDC a Jihar Gombe ta ce ta shirya tsaf don tunkarar zabubbukan bana da za a fara a gobe Asabar.
Kwamandar Hukumar ta Jihar, Hajiya Altine Sani Umar ce ta bayyana haka a shekaranjiya Laraba lokacin da take ganawa da manyan jami’an hukumar don isar da sakon Babban Kwamandansu na Kasa Alhaji Abdullahi Gana Muhammad, cewa ba za su gajiya ba wajen tabbatar da tsaro don ganin zaben ya gudana cikin lumana.
Ta ce a shirye suke kan aikin, abin da suke fata shi ne a samu sahihin zabe ba tare da tashin tashina ba. Ta ce kimanin jami’ai sama da 700 ne hukumar ta ware a Jihar Gombe don gudanar da aikin zabe tare da hadin guwiwar ’yan sanda.
A cewarta, yanzu haka jami’anta ne suke yi wa ma’aikatan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) rakiya wajen rarraba kayayyakin zabe da aka kawo daga filin jirgin saman Gombe da ke garin Lawanti zuwa kananan hukumomin jihar 11.
Hajiya Altine ta kara da cewa ba a fatar tashin hankali amma idan ya faru jami’anta za su dauki mataki a kan duk wanda ya ta da tarzoma a lokacin zaben. Ta ce don ganin an kara inganta tsaro, Mataimakin Kwamandansu na Kasa da ke Shiyyar Bauchi, zai zo Gombe a ranar zaben don tauna tsakuwa aya ta ji tsoro.
Daga nan sai ta shawarci masu zabe cewa a yi zabe cikin lumana, a guje wa tashin hankali domin duk wanda ya ta da rikici a lokacin zaben ba za su bar shi ba, doka za ta yi aikinta a kansa.