Hukumar SEMA ta Filato ta tallafa wa mutanen Jingir
Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Filato (SEMA) ta tallafa wa wadanda ruwa ya yi wa gyara a kwanakin baya a garin Jingir da ke karamar Hukumar Bassa da kayan abinci da na gini. Ruwan da iska sun yaye rufin gidaje sama da 300 a lokacin.Da yake mika kayayyakin Sakataren Hukumar (SEMA) Alhaji Alhassan Barde ya […]

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Filato (SEMA) ta tallafa wa wadanda ruwa ya yi wa gyara a kwanakin baya a garin Jingir da ke karamar Hukumar Bassa da kayan abinci da na gini. Ruwan da iska sun yaye rufin gidaje sama da 300 a lokacin.
Da yake mika kayayyakin Sakataren Hukumar (SEMA) Alhaji Alhassan Barde ya ce gwamnatin jihar na iyakar kokarinta wajen tallafa wa wadanda wata annoba ta auku musu, kuma wannan ne ya sa ta tallafa wa al’ummar Jingir da kayan abinci da na gini.
Ya ce kayayyakin sun hada da buhunan shinkafa 50 da na wake 50 da na masara 100 da na gishiri 30 da jarkokin manja 30 da katifu 400 da barguna 700 da tabarmi 700 da sabulai katan 20 da bardir din kwanon rufi 200 da katan-katan na kusa da buhunan siminti 100.
Ya yi kira gare su kan su yi amfani da su yadda ya kamata, kuma ya yi kira ga al’ummar jihar su ba gwamnatin jihar goyon baya kan wannan kokari da take yi, tare da kai rahoton faruwar annoba ga hukumar domin daukar mataki.
Shugaban riko na kkramar hukumar Mista Andrew Bari Iza ya ce tallafin da gwamnatin jihar ta kawowa al’ummar garin ta hannun Hukumar SEMA, ya nuna cewa lallai gwamnatin jihar tana damuwa da mawuyacin hali da al’ummar jihar suka shiga. Don haka ya yaba wa Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang kan wannan kokari.
A jawabin basaraken yankin, Ogomo na Pengana Mista Isa’ac Sambo ya mika godiyarsu ga Gwamna Jonah Jang kan tallafi da aka kawo wa al’ummar yankin na Pengana. Kuma ya yaba wa shugaban karamar kan tallafawa wadanda bala’in ya shafa a lokacin da ya faru.