Hukumar SEMA ta Gombe ta tallafa wa ’yan gudun hijira 73 daga Borno da Filato

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta ba mutum 73 daga jihohin Borno da Filato da rikice-rikice suka shafa suke gudun hijira a jihar tallafi.Sakataren Hukumar SEMA Mista Kelmi John Lazarus ne ya bayyana haka a Gombe a lokacin da yake jagorantar Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Alhaji Jalo Abubakar Bajoga […]

Hukumar SEMA ta Gombe ta tallafa wa ’yan gudun hijira 73 daga Borno da Filato

 Irin kayayyakin da aka ba ‘yan gudun hijira a GombeHukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta ba mutum 73 daga jihohin Borno da Filato da rikice-rikice suka shafa suke gudun hijira a jihar tallafi.
Sakataren Hukumar SEMA Mista Kelmi John Lazarus ne ya bayyana haka a Gombe a lokacin da yake jagorantar Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Alhaji Jalo Abubakar Bajoga wajen ba da kayayyakin tallafin.
Mista Kelmi J. Lazarus, ya ce an ba da tallafin ga ’yan gudun hijirar ne domin a rage musu radadin kuncin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki.
Shi kuwa Kwamishina Jalo Abubakar Bajoga, cewa ya yi wannan kaya da suke tallafa wa mutanen tallafi ne daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Gombe.
Alhaji Jalo Bajoga ,ya ce sun gayyaci jami’an tsaro na farin kaya da na Cibil Defence da jami’an Hukumar Kiyaye Haddura da sojoji da sauransu domin sanya ido kan kayan da za a raba domin ganin ba a samu matsala a lokacin rabon ba.
Jami’in Hukumar NEMA a Jihar Gombe Mista Apolos ya ce ya zama dole su halarci wurin da ake raba kayan da kansu don ganin an raba kayan ga wadanda aka kawo dominsu.
daya daga cikin wadanda suka samu tallafin mai suna A’isha Usman ’yar asalin garin Jere a Jihar Borno ta bayyana jin dadi kan tallafin, inda ta ce rikice-rikicen da suke faruwa a jiharsu ne ya sa suke gudun hijira a Gombe don tsira da rayuwanrsu.
Ta ce a yanzu watansu biyu a Gombe suna fake a wurin wasu ’yan uwansu, kuma suna fatar komawa garuruwansu a duk lokacin da hankali ya kwanta
Kayayyakin da aka ba su sun hada da katan-katan na taliyar Indomi da katifu uku-uku da tabarmi da bukatan roba da kayan masarufi da sauran kayayyakin aikin gida da sauransu.