Hukumar Shari’a ta dakatar da ma’aikatan kotu kan badaƙalar filaye a Kano
Badaƙalar filaye ta sa an dakatar da Magatakardan kotu ba tare da albashi ba
Hukumar Shari’a ta jihar Kano (JSC) ta ladabtar da wasu Magatakardan Kotunan Musulunci biyu kan badaƙalar filaye.
Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya sanar cewa ɗaukar matakin ya zo ne a yayin taron hukumar karo na 75 da aka gudanar a ranar 12 ga watan Satumbar nan da muke ciki.
Ya ce hakan na zuwa ne bayan kwamitin bincike da aka kafa kan ƙorafin da aka yi a kansu ya miƙa rahotonsa.
Binciken ya gano cewa Jamilu Ibrahim tare da waɗanda suka haɗa baki sun karɓi kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba, suka bayar da takardar mallakar fili ta hanyar yaudara, domin siyar da wasu filaye guda biyu.
- An tsinci gawa a rataye cikin makarantar Islamiyya a Jigawa
- An jefa mu cikin tashin hankali da rufe sansanonin ambaliya —’Yan gudun hijira
Hakan ce tasa kwamitin ya ba da shawarar a kori Jamilu Ibrahim daga aiki, amma hukumar shari’a ta dakatar da shi ba tare da biyan albashi ba har sai an kammala shari’ar da yake fuskanta a gaban kotun Majiatare.
Shi kuma Zubairu Sulaiman, wanda magatakardan Babbar Kotun Musulunci ne, an same shi da karɓar Naira miliyan ɗaya ta asusunsa na ƙashin kansa a matsayin la’ada bayan siyar da filayen guda biyu.
A don haka ne shi ma Hukumar shari’a ta dakatar da shi na tsawon watanni huɗu ba tare da biyan albashi ba, kamar yadda kwamitin binciken ya bayar da shawara.
A ƙarshe hukumar ta jaddada aniyarta na tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da hukuncin da ya dace, kan duk ma’aikaci da ya aikata ba daidai ba musamman waɗanda aka ɗora wa alhakin gudanar da shari’a, don kare mutunci da riƙon amanar ɓangaren shari’a da ma tabbatar da amincewar jama’a.