Hukumar Shari’a ta fara farautar wadanda suka kafa kungiyar ’yan luwadi a Bauchi
Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta bayyana niyyarta na farauto ’yan luwadi 168 da suka ce sun kafa kungiya tare da samun tallafin wata babbar kungiyar ’yan luwadi ta kasar Amurka wacce ta ba su gudunmawar Naira miliyan biyar don ci gaba da neman mambobi a kananan hukumomi 20 na jihar.Shugaban Hukumar Malam Mustapha […]

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta bayyana niyyarta na farauto ’yan luwadi 168 da suka ce sun kafa kungiya tare da samun tallafin wata babbar kungiyar ’yan luwadi ta kasar Amurka wacce ta ba su gudunmawar Naira miliyan biyar don ci gaba da neman mambobi a kananan hukumomi 20 na jihar.
Shugaban Hukumar Malam Mustapha Baba Ilelah ne ya bayyana haka ga taron manema labarai da ya kira a ofishinsa a ranar Talata, inda ya yi Allah wadai tare da nuna fushin hukumar kan wani labari da jaridar Hausa Leadership ta rubuta. Labarin ya ruwaito cewa ’yan kungiyar sun yi taron kafa kungiyar a wani otel da ke unguwar GRA a Bauchi inda suka gayyaci wakilin jaridar bisa dalilin ita ce kawai za ta iya yayata manufofinsu.
Malam Mustapha Ilelah ya nuna bacin rai tare da bayar da hakuri ga al’ummar Jihar Bauchi game da wannan labari wanda ya kira a matsayin cin zarafi ga al’ummar jihar Musulmi da Kirista.
Ya ce sun himmatu wajen ganin sun farauto shugabannin kungiyar ta ’yan luwadi a karkashin shugabansu Baballe Sale da sauran shugabannin da suka hada da Paul Yali da Injiniya Salisu Garba da Uba Babangida da Sirajo Bello Yalwa da Abba Uba da Barista Sani wanda shi ne lauyan kungiyar kamar yadda Jaridar ta zano sunayensu da matsayinsu a fitowarta ta Juma’ar da ta wuce.
Malam Baba Ilelah ya yi tir da wannan kungiya tare da neman jama’a su la’anci aniyarsu da kuma lura da take-taken matasa. Ya ce a duk lokacin da suka ga alamun wanzuwar ayyukan kungiyar a ko’ina a sanar da su, ya ce saboda ya sabawa dokokin shari’a na 8 sashe na 133 na Jihar Bauchi wanda ya haramta wannan aiki kuma duk wanda ya aikata hukumar zata gurfanar da shi gaban kotu domin ya amsa laifisa.
Shugaban ya roki ‘yan jarida su rika amfani da kwarewa yayin gudanar da aikin su don kare martabar aikin da ta jama’ar da suke wakilta da kuma kafar da suke wa aiki. Yace sun yi dukkan kokari don wakilin mai suna Hamza Aliyu yazo ya karawa hukumar bayani amma bai zo ba, don haka yanzu suka himmatu wajen gano wadannan mutane kuma sun fara samun nasarar jin inda suke, tare da cewa gaskiyane sun yi wannan taro sun kafa kungiyar kuma sun dukufa suna neman mambobi kan wadanda suke da su, don haka yace aikin hukumar ne ta dakile duk wani fasidi a Jihar Bauchi, kuma tuni za su yi aiki da jami’an tsaro don ganin wannan kungiya bata samu kafuwa da tasiri a Jihar Bauchi ba don tsarkake al’umma.