Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta kama ’yan kungiyar luwadi 11
Shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci a Jihar Bauchi Malam Mustapha Baba Ilela ya yaba game da irin addu’o’in da mutane suka yi a wuraren ibada domin amsa kiran hukumar na la’antar ayyukan ’yan luwadi da suka ce sun kafa kungiyarsu a jihar kwanakin baya. Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da wakilinmu bayan samamen da […]
Shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci a Jihar Bauchi Malam Mustapha Baba Ilela ya yaba game da irin addu’o’in da mutane suka yi a wuraren ibada domin amsa kiran hukumar na la’antar ayyukan ’yan luwadi da suka ce sun kafa kungiyarsu a jihar kwanakin baya. Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da wakilinmu bayan samamen da ’yan Hisbah da jami’an tsaro suka kai kan ’yan kungiyar suka kama mutum 11 daga cikinsu, ciki har da mataimakin shugaban wata makarantar sakandare, inda a halin yanzu aka kai su Babbar Kotun Shari’a ta Biyu da ke Unguwar Jaki. Malam Baba Ilela ya ce ana tsare da mutum 11 akwai daya da ake magana a kansa saboda ba a samu cikakkiyar shaida daga ’yan kungiyar a kan cewa shi ma mambansu ne ba. Ya ce samun labarin kafuwar kungiyar ke da wuya suka raba wasiku zuwa ga limaman masallatai da shugabannin jama’a inda mutane suka bayar da hadin kai suka yi ta buga musu waya suna tona asirin wadanda suka sani, har aka kamo su suka bayar da sunan wadanda suka jefa su a cikin kungiyar. Ya ce har zuwa wannan lokaci ba a samu nasarar cafke shugabanta ba saboda ba a cikin Bauchi yake da zama ba. Shugaban ya yaba wa al’ummar jihar kuma ya nemi shugabannin kananan hukumomi da jami’an tsaro da limamai da shugabannin jama’a su sa ido domin gano ’ya’yan kungiyar da masu alaka da ita don ganin ba ta samu kafuwa ba a jihar. Game da mata ’yan madigo da suka ce sun kafa tasu kungiyar ya nemi mata su taimaka wajen sa ido tare da tona asirin duk wanda aka sani na yunkurin kafa irin wannan kungiya don a dakile ta, saboda a inganta tarbiyyar matasa wacce ta shiga mawuyacin hali a wannan lokaci.