Hukumar Shari’a ta nemi Musulmi su rika warware matsalolinsu a masallatai
Shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi Malam Mustapha Baba Ilelah ya shawarci Musulmi su mayar da masallatai wurin da za su rika tattaunawa domin magance matsalolinsu na yau da kullum da suka shafi jama’a ba tare da sai an fita zuwa gaban hukumomi ba.Shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron bude Masallacin Juma’a […]
Shugaban Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi Malam Mustapha Baba Ilelah ya shawarci Musulmi su mayar da masallatai wurin da za su rika tattaunawa domin magance matsalolinsu na yau da kullum da suka shafi jama’a ba tare da sai an fita zuwa gaban hukumomi ba.
Shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron bude Masallacin Juma’a na Unguwar Zango Federal Lowcost da aka yi ranar Juma’ar da ta gabata.
Malam Mustapha Ilelah ya shawarci limamai da na’ibansu da sauran jagorori su kasance masu hakuri da jama’a ta hanyar hada kai da mutanen da ake zaune da su domin bunkasa masallatan musamman na Juma’a saboda su kasance cibiyoyin da za a rika tattauna lamuran da suka shafi jama’a kamar yadda ke faruwa a wasu kasashen Musulmi.
Ya ce ta hanyar irin wannan tattaunawa ce za a samu magance matsalolin da suka shafi jama’a a unguwa da yankunansu domin samar da maslaha ga al’umma shi ne aikin Annabawa, kuma malamai su ne magada Annabawa wajen isar da sakon ubangiji.
Wazirin Zango Malam Gambo danladi wanda ya wakilci Mai Unguwar Zango ya gode wa jama’ar da suka halarci bude masallacin ne da wadanda suka taimaka wajen gina shi, inda ya shawarci jama’ar unguwar su zauna da juna lafiya musamman matasa.
Malam Yunusa Ado wanda ya wakilci Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Bauchi a jawabinsa ya nemi jama’a su zauna da juna lafiya kuma su yi kokari bunkasa harkokin addini a masallacin.