Hukumar Sibil Difens za ta ɗauki sabbin jami’ai

Shugaban ƙasa ya sahale wa hukumar ta Sibil Difens ta ɗauki sabbin jami’ai

Hukumar Sibil Difens za ta ɗauki sabbin jami’ai

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta samu sahalewar Shugaban Ƙasa na ƙara daukar sabbin ma’aikata.

Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Aifi, na ya sanar da haka, a yayin ƙaddamar da Baban Ofishin Yanki na Hukumar a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya a ranar Laraba.

“Nan gaba kaɗan za mu ɗauki ’yan Najeriya masu kyawawan ɗabi’u a matsayin jami’ai a Sibil Difens, kuma muna godiya ga shugaban ƙasa bisa wannan dama da ya ba hukumar,” in ji shi.

Ya bayyana cewa Hukumar ta fara shirye-shiryen ɗaukar sabbin, amma sai nan gaba za ta sanar da ranar fara ɗaukar tasu.

Ya kuma yaba wa Majalisar Ƙaramar Hukumar Bwari bisa gina ofishin, wanda ya ce zai taimaka wajen inganta tsaro.

Olusola Odumosu, wanda shi ne Kwamandan Hukumar, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar, John Gabata da ya samar da ofishin cikin kyakkyawan yanayi ga jami’an hukumar tsaron.