Hukumar SSS na fuskantar matsi kan kashe tsararru a hedkwatarta

Hukumar Tsaron kasa (SSS) tana fuskantar tambayoyi kan yadda aka kashe tsararru 21 a lokacin yunkurin gudu daga hedkwatarsu, inda ake zargin an boye gaskiyar lamari ga jama’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.An ruwaito cewa tsararrun da ake zargi ’yan Boko Haram ne sun mutu ranar Lahadin da ta gabata bayan […]

Hukumar SSS na fuskantar matsi kan kashe tsararru a hedkwatarta
Hukumar SSS na fuskantar matsi kan kashe tsararru a hedkwatarta

Hukumar Tsaron kasa (SSS) tana fuskantar tambayoyi kan yadda aka kashe tsararru 21 a lokacin yunkurin gudu daga hedkwatarsu, inda ake zargin an boye gaskiyar lamari ga jama’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
An ruwaito cewa tsararrun da ake zargi ’yan Boko Haram ne sun mutu ranar Lahadin da ta gabata bayan daya daga cikinsu ya kwace bindiga daga wani mai gadinsu.
Kakakin Hukumar SSS Marilyn Ogar ta shaida wa wani gidan rediyo cewa dukkan wadanda aka kashen jami’an SSS ne suka kashe su. Sai dai ta ce ana ci gaba da bincike don gano wa ya harbi wa kuma a kan me kuma mutane nawa aka harba kuma wa ya harbe su, sannan a dalilin me.
Ogar ta ce bindigar da tsararren ya kwace tana shake da harsasai 90 kuma ya yi ta harba ta ba kakkautawa.
Ta ce karar harbe-harbe ta kusan awa daya da aka rika ji a hedkwatar SSS da zagayenta na gargadi ne ko da tsararrun suna da mataimaka.
Da Aminiya ta tuntubi Ogar ta yi bayani kan hakikanin abin da ya jawo mace-macen, ta ki cewa komai. Sannan fadar Shugaban kasa ta kawar da kai kan lamarin, yayin da kafofin watsa labarai suka rika nuna shakku kan bayanan mahukunta game da lamarin.