Hukumar SSS ta nuna wadanda ake zargi da kashe Albani
Hukumar Tsaron kasa (SSS), ta nuna mutum bakwai da ake zargin ’yan Boko Haram kuma ake zarginsu da hannu a kashe fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Zariya Sheikh Muhammad Awwal Adam Albani.Kakakin Hukumar SSS, Marilyn Ogar ne ta nuna wadanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin […]
????????????????????????????????????

Hukumar Tsaron kasa (SSS), ta nuna mutum bakwai da ake zargin ’yan Boko Haram kuma ake zarginsu da hannu a kashe fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Zariya Sheikh Muhammad Awwal Adam Albani.
Kakakin Hukumar SSS, Marilyn Ogar ne ta nuna wadanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata.
Wasu ’yan bindiga ne suka kashe Sheikh Albani da matarsa da dansa a Zariya a ranar 1 ga Fabrairun da ya gabata a lokacin da yake komawa gida daga karantarwa.
A kwanakin baya Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani faifan bidiyo inda ya yi da’awar kungiyar ce ta kashe malamin, sai dai almajiran Sheikh Albani sun yi watsi da da’awar, inda suka ce ana amfani ne da wannan suna domin boye hakikanin wadanda suka yi aika-aikar.
Ogar ta ce wadanda aka kama sun yi ikirarin kashe Sheikh Albani, kuma ta ce an kama su ne tsakanin 13 da 21 ga Fabrairun da ya gabata.
Ta ce wadanda aka kama sun hada daYakubu Abdullahi (mai shekara 42), wanda ta bayyana da wanda ya tsara kisan kuma kwamandan kungiyar a jihohin Kaduna da Neja.
Sauran wadanda aka kama a cewar Ogar sun hada da Yasir Ibrahim (mai shekara 35), wanda ya karanta digiri na farko kan adabin Ingilishi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sai Ibrahim Shu’aibu mai shekara 22 da Bilyaminu Usman mai shekara 22 da Sahabi Isma’il, mai shekara 27 da Umar Farouk Isma’il mai shekara 35 da kuma Musa Abubakar mai shekara 54.
A cewar SSS Yakub Abdullahi yana cikin harkokin kungiyar dumu-dumu tun rikicin da ya auku lokacin fafatwar jami’an tsaro da hukumomin tsaro a Maiduguri a shekarar 2009.
Ta ce, “Bincike da ikirarin da wadanda ake zargi suka yi sun nuna cewa goyon bayan ilimin zamani da fasalin wa’azinsa da ya saba da akidar Boko Haram ne suka jawo kaiyayyarsu gare shi, har suka yi taro a karkashin Yakub Abdullahi a Hayin danmani da ke yankin Rigasa. Kuma a wurin ne Abdullahi ya ce Majalisar Shura – wadda ita ce babbar majalisar Boko Haram – ta bayar da umarnin a kashe Albani.”
Ogar ta ce an yi yunkurin hallaka malamin a ranar 24 ga Janairu. “Sai aka rika kiwonsa, inda a ranar 1 ga Fabrairu ’yan Boko Haram suka bi shi Cibiyar Markaz Salafiyya. Sun jira shi har karshen darasinsa, suka bi shi a karshe suka kashe shi tare da matarsa da dansa,” inji ta.
Kakakin ta ce an yi amfani da bindiga kirar AK 47 guda biyu wajen kashe malamin, kuma an kawo bidigogin ne daga Katsina. Ta ce mutum na uku da ake zargi Bilyaminu Usman ya harbi malamin da matarsa da dansa sau 30.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai cikin harshen Hausa Abdullahi ya yi ikirarin kisan. Ya ce an kashe Albani ne bisa umarnin Majalisar Shura. Shi ma Yasir Ibrahim wanda ya fito daga karamar Hukumar Birnin Kano ya yi ikirarin zama dan kungiyar. Sai dai ya ce ba da shi aka yi kisan ba, amma da shi aka tsara. Ya ce, “Akwai lokacin da Albani ya ce zai kashe duk wani dan Boko Haram kuma ya hada kai da hukumomin tsaro…”
Ya kara da cewa, “Akwai lokacin da aka samu rikici tsakanin Albani da wasu daliban Al- Zakzaky sai suka kashe wani wanzami, saboda sun ce duk wanda ya zo kusa da gidansu za su kashe shi. dalibansa sun kama wannan wanzami kuma aka yanka shi.”
Ogar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu yayin da za a ci gaba da gudanar da bincike don zakulo sauran wakilan kungiyar da suke zaune a jihohin Kaduna da Neja.
An samu bayanin cewa Ibrahim Shu’aibu wanda ya fito daga Rimin Gado a Jihar Kano ya shiga kungiyar Boko Haram ne a shekarar 2008 a matsayin mai nema mata goyon baya a Zariya. Kuma shi da Yasir Ibrahim ne suka kawo bindigogin da aka yi amfani da su daga Funtuwa zuwa Zariya.
….A kotun Musulunci ya dace a gurfanar da makasan Albani -Kakakin dalibansa
Daga Aliyu Babankarfi, Zariya
Dokta Abdulganiyu Abdulrafi’u malami ne a fannin kimiyyar kasa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya kuma shi ne kakakin daliban marigayi Sheikh Muhammad Awwal Adam Albani. Ya bayyana wa Aminiya matsayinsu game da wadanda jami’an tsaro suka nuna suka ce su ne suka kashe Albani. daliban Albani sun sha karyata cewa ‘yan Boko Haram ne suka kashe malamin nasu. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Da yake yanzu jami’an tsaro na farin kaya sun nuna mutane bakwai da suke zargi da kisan malamin, me za ka ce a kan haka?
To, dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mu da ma mun dade muna jiran irin wannan dama da gwanati za ta fito ta ce ‘yan Boko Haram ne suka kashe Malam (Sheikh Albani). Abu na farko da nake so ka sani shi ne, addinin Musulunci addini ne wanda yake da tsari, addini ne wanda yake karfafa mabiyansa da su nemi ilimi kowane iri, har da na Boko, don su zama ba a bar su a baya ba a dukkanni harkokin rayuwa. Wannan matsayi na addinin Musulunci shi ne dalilin da ya sa malaminmu ya yi ta karfafa mu don shiga kowadanne irin harkokin rayuwa.