Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Hukumar ta soke lasisin jarumar tare da hana ta fitowa a cikin fim na tsawon watanni 12.

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, kan karya dokokin hukumar da suka shafi shigar banza da wallafa abubuwan da ba su dace ba.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ya ce hukumar ta gargaɗi Samha a lokuta da dama kan “shigar banza da bayyana tsiraici,” amma ta ƙi bin doka.

Saboda haka, hukumar ta yanke hukuncin dakatar da ita.

Dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take, ta haramta wa Samha fitowa a kowane fim na tsawon watanni 12 masu zuwa.

Haka kuma, hukumar ta soke lasisin jarumar, tare da daina tantance fina-finan da ta fito a ciki.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon ƙorafe-ƙorafen da al’ummar Kano suka yi a kan halayen jarumar da suka saɓa wa dokokin hukumar.

Wannan mataki yana ɗaya daga cikin yunƙurin jagorancin hukumar, ƙarƙashin Abba Al-Mustapha, na dawo da tsari da ƙwarewa a masana’antar fina-finan Hausa.