Hukumar Tara Kudin shiga ta tara fiye da tiriliyan biyu a wata takwas
Hukumar Tara Kudin Shiga ta Kasa ta karbi kimanin Naira tiriliyan biyu da rabi a cikin watanni takwas na shekarar da muke ciki. Wani kundi da Aminiya ta sami kwafinsa ya nuna cewa mafiyawan kudin ya fito ne daga harajin ribar mai wanda hukumar ta karbi Naira tiriliyan da digo bakwai sannan kuma harajin da ta […]

Hukumar Tara Kudin Shiga ta Kasa ta karbi kimanin Naira tiriliyan biyu da rabi a cikin watanni takwas na shekarar da muke ciki.
Wani kundi da Aminiya ta sami kwafinsa ya nuna cewa mafiyawan kudin ya fito ne daga harajin ribar mai wanda hukumar ta karbi Naira tiriliyan da digo bakwai sannan kuma harajin da ta karba daga bangarorin da ba na mai ba ya kai fiye da biliyan dari 876.
A watan Janairu kawai, Hukumar ta karbi fiye da Naira biliyan 317 a watan Fabarairu ta tara fiye da Naira biliyan 229 a watan Maris ta karbi fiye da Naira biliyan 230 sai kuma a watan Afrilu ta karbi fiye da Naira biliyan 218.
A watan Mayu kudin da hukumar ta tara ya kai fiye da biliyan 286 haka a watan Juni hukumar ta samu fiye da Naira biliyan 500 sai kuma a watan July inda hukumar ta sami fiye da Naira biliyan 328 sannan kuma a watan Agusta ta tara fiye da Naira biliyan 396.