Hukumar Tashoshin Jiragen Sama za ta yi maganin ’yan baranda
Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Najeriya ta ce ta gaji da zubar da mutuncin da ’yan baranda ke yi ga tashoshin jiragen saman kasar nan wajen tafiyar da harkokinsu a filayen jiragen saman.Kakakin Hukumar Yakubu Datti ya shaida wa taron manema labarai a Legas cewa sun gargadi ’yan barandar ya fi shurin masaki […]
Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Najeriya ta ce ta gaji da zubar da mutuncin da ’yan baranda ke yi ga tashoshin jiragen saman kasar nan wajen tafiyar da harkokinsu a filayen jiragen saman.
Kakakin Hukumar Yakubu Datti ya shaida wa taron manema labarai a Legas cewa sun gargadi ’yan barandar ya fi shurin masaki kan su bar tashoshin jiragen ko su nemi sana’ar kwarai maimakon sanya fasinjoji a cikin matsala.
Ya ce ba zai yiwu hukumar tana aiki domin inganta harkoki a tashoshin jiragen saman har Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Duniya ta ba ta lambar yabo, amma wasu su nemi bata mata aiki da rana tsaka ba. Ya ce wannan ne ya sa suka samar da kotun tafi-da-gidanka domin hukunta duk wanda aka samu yana cuwa-cuwa ko zama dan baranda a tashoshin jiragen saman.
Yakubu Datti ya tabo shirin nan na fita da kayan gwari zuwa kasashen waje ciki har da kasashen Turai, inda ya ce nan da ’yan kwanaki manoma za su fara fitar da tumatir da tattasai da albasa da sauransu domin sayar wa kasashen.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta kammala tsarin kuma za ta agaza wa manoma a wannan fanni, domin magance rubewar kayan lambu da manoman kasar nan ke fuskanta.
Yakubu Datti ya ce a karkashin wannan tsari kwanan nan jiragen fasinja na kasa da kasa za su fara sauka a Enugu, ya ce suna fata haka ya kara samar da ayyukan yi a cikin kasa da kuma kara samun kudin shiga ga jama’a.