Hukumar tsaro ta NSCDC ta tallafawa marayu 33 a Jihar Katsina
A makon jiya ne Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Katsina ta tallafa wa marayu sama da 30 da suka rasa mahaifansu a lokacin da suke aiki a karkashin hukumar.A lokacin da yake mika tallafin ga iyalan mamatan, Kwamandan Hukumar ta Jihar Katsina Ibrahim Musa Zabura ya ce wannan tsari na gidauniyar tallafa […]

A makon jiya ne Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Katsina ta tallafa wa marayu sama da 30 da suka rasa mahaifansu a lokacin da suke aiki a karkashin hukumar.
A lokacin da yake mika tallafin ga iyalan mamatan, Kwamandan Hukumar ta Jihar Katsina Ibrahim Musa Zabura ya ce wannan tsari na gidauniyar tallafa wa iyalan jami’an hukumr da suka rasu a lokacin da suke aiki shi ne na farko da hukumar ta bullo da shi.”In za mu lura yara da dama a duniya marayu ne wanda hakan ya nuna cewa, lallai wata rana mu ne za mu tafi mu bar iyalanmu. A kan haka ina yaba wa wadanda suka yi tunanin kirkiro da wannan gidauniya domin tallafa wa wadannan yara da suke ’ya’yanmu ne.”
Kwamanda Zabura yayi kira ga wadanda nauyin kula da marayun ke kansu su tabbatar sun tsare su a kan ci gaba da addinansu da tarbiyyarsu tare da karatunsu. Har ila yau, ya yi kira ga masu hannu da shuni su rika shigowa don tallafawa irin wadannan marayu da kan rasa mahaifansu a lokacin da suke aikin bauta wa kasa da al’ummarta. Sai Kwamandan ya dauki nauyin yi wa marayu 16 maza da mata kayan Sallah.
Malam Adamu Yusuf daya daga cikin jami’an rundunar masu wa’azi tunatarwa ya yi a kan muhimmancin tallafa wa marayu, inda ya kawo ayoyi da Hadisai da suka yi magana a kan marayu da tallafa musu.
daya daga cikin waliyyan marayun da suka samu tallafin Malam Bashir, ya nuna godiyarsu ga jami’an hukumar a kan tallafin da suka yi wa yaran, tare da tabbatar da cewa za su yi iya kokarinsu na rike wannan amana.
An raba wa marayu 33 Naira dubu 70 nan take, tare da kokarin sake kafa wani asusun bayar da tallafin yau da kullun ga jami’an hukumar.
In dai za a iya tunawa, wannan runduna ta sha bayar da irin wannan tallafi ga gidajen marayu da masu ciwon yoyon fitsari da ke Jihar Katsina.