Hukumar tsaron NSCDC ta sa ido wajen rarraba man fetur

Bayan share shekaru da dama Daffon mai na Gombe ba ya aiki a karon farko hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar ta sa ido wajen fara rarraba mai daga daffon zuwa wasu jihohin Arewa maso gabashin Najeriya. Kwamandar hukumar a Jihar Gombe, Hajiya Altine Sani Umar, ita ta bayyana hakan a Gombe a […]

Hukumar tsaron NSCDC ta sa ido wajen rarraba man fetur

Bayan share shekaru da dama Daffon mai na Gombe ba ya aiki a karon farko hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar ta sa ido wajen fara rarraba mai daga daffon zuwa wasu jihohin Arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamandar hukumar a Jihar Gombe, Hajiya Altine Sani Umar, ita ta bayyana hakan a Gombe a lokacin da take zantawa da manema labarai, inda ta ce hakkinsu ne su sa’ido wajen ganin an rarraba man zuwa sauran makwaftan jihohin ba tare da an karkatar da shi ba.

Hajiya Altine Sani Umar, ta ce manufar sa’idon nasu shi ne su tabbatar da man fetur din ya isa duk fadin jihar inda aka tura ta ba tare samun kowanne irin cikas ba.

Ta kuma ce an fara aikin rarraba man fetur din ne a ranar Litinin da ta gabata, kuma duk tankunan da suka bar Gombe zuwa wata jiha sun isa lafiya.

Har ila yau ta kara da cewa hukumar ta kama wasu mutane takwas da laifuffuka daban-daban, inda wasu masu motoci suke kara tankunansu da suke cin lita dubu uku don karkatar da man da suka sha.

Sannan sai ta yi kira ga daukacin al’umma da cewa su guji aikata irin wannan laifuffuka.

“A matsayin mu na jami’an tsaro ba zamu zuba ido muna gani ana karya doka ba sai mun tabbatar da masu laifi sun fuskanci doka”. Inji Altine.

Ganin Daffon na Gombe ya jima baya raba mai sai yanzu wakilinmu ya yi ta kokarin jin ta bakin manajan Daffon Ibrahim Muhammed, da ma masu ruwa da tsaki hakan ya ci tura, inda duk bangaren da muka tuntuba sai su ki cewa komai.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50