Hukumar UNOCHA ta shirya taron kara wa juna sani na kwana biyu a kan HRP
A ci gaba da kokarinta na kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye mutanen yankin Arewa Maso Gabas, Ofishin kula da ayyukan ji kai na Majalisar dinkin Duniya (UNOCHA) ya shirya tsaf domin aiwatar da taron kara wa juna sani na kwana biyu mai taken “Shekarar 2018, ayyukan jin kai da tsara ayyuka a yankin Arewa […]
A ci gaba da kokarinta na kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye mutanen yankin Arewa Maso Gabas, Ofishin kula da ayyukan ji kai na Majalisar dinkin Duniya (UNOCHA) ya shirya tsaf domin aiwatar da taron kara wa juna sani na kwana biyu mai taken “Shekarar 2018, ayyukan jin kai da tsara ayyuka a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.”
Taron kara wa juna sanin zai gudana ne a Otel din Bolton White da ke Garki Abuja a ranukan 11 da 12 na watan Oktoban bana. Daga cikin wadanda za su halarci taron akwai PCNI, Hukumar NEMA, ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare, gwamnati da Hukomomin UN, Babban Bankin Duniya da kuma masu bayar da tallafi daga kungiyoyin bayar da agaji da ci gaba.
Taron zai yi dubi ne a kan yadda ake tafiyar da ayyukan jinkai a jihohi shida na yankin Arewa Maso Gabas, sannan kuma ya yi gyare-gyare a inda ya kamata, sannan kuma taron zai yi dubi da yadda gwamnatin kasa da na kasashen duniya suke taimakawa wajen ayyukan jinkai a yankin a bana, da kuma matsalolin da ake samu wajen isar da kayyaykin jinkan, da kuma tsara yadda za a yi a badi. Taron kuma zai shirya yadda za a tsaftace ayyukan jinkan ta hanyar shirya ayyukan ci gaba mai dorewa.