Hukumar USAID da SUWASA za su inganta samar da ruwan sha a Jihar Bauchi

Hukumar Bunkasa kasashe ta kasar Amurka (USAID) da ofishin inganta samar da ruwan sha (SUWASA), sun kulla yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Bauchi domin samar da tsaftttacena ruwan sha a jihar.Shugaban shirin a Jihar Bauchi Injiniya Hosanna Dajan ne ya bayyana haka a wajen taron masu ruwa da tsaki a harkar samar da ruwan sha da […]

Hukumar USAID da SUWASA za su inganta samar da ruwan sha a Jihar Bauchi
Hukumar USAID da SUWASA za su inganta samar da ruwan sha a Jihar Bauchi

Hukumar Bunkasa kasashe ta kasar Amurka (USAID) da ofishin inganta samar da ruwan sha (SUWASA), sun kulla yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Bauchi domin samar da tsaftttacena ruwan sha a jihar.
Shugaban shirin a Jihar Bauchi Injiniya Hosanna Dajan ne ya bayyana haka a wajen taron masu ruwa da tsaki a harkar samar da ruwan sha da kuma shugabannin jama’a da Hukumar SUWASA ta shirya a Bauchi.
Injiniya Hosanna Dajan, ya ce aikin ofishinsa shi ne samar da ruwan sha mai tsabta a Afirka, kuma sun shirya taron ne don gano hanyoyin wayar da kan jama’a su gane sauye-sauye da ake son yi ta fuskar samar da ruwan sha ga al’umma.
Ya ce a karkashin SUWASA, gwamnatin Amurka take bayar da tallafi ga kasashe masu tasowa don samun hanyar inganta samar da ruwan sha.
Ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar da hadin kai da duk abin da ake bukata don samun nasarar shirin musamman a cikin birane inda mutane suke cunkushe, tare da yawan bukatar ruwan sha.
Babban jami’i mai kula da shirin wayar da kai na SUWASA Injiniya Rabi’u Almustapha ya ce mutane suna sha’awar shirin inganta samar da ruwan sha ta hanyar tallafa wa gwamnatin jihar domin inganta ruwan sha a garuruwan da jama’arsu suka wuce mutum dubu 20.
Ya ce shirin zai duba matsalolin mutanen da suke zaune a birane saboda yadda ruwan da ake da shi a kasa yake gurbacewa saboda karuwar masai a cikin birane.
Injiniya Rabiu ya ce ya kamata jama’a su fahimci lokaci ya yi da za a daina dogaro kan gwamnati ta fuskar samun ingantaccen ruwan sha. Ya ce kullum ana kashe kudi a kan samar da ruwan sha, amma babu ruwan don haka yanzu aka kawo sabon sauyi, inda hukumar ruwa ta jihar za ta samu ’yancin gudanar da ayyukanta, ta yadda duk kudin da aka sanya a hanyar samar da ruwan sha zai yi tasiri bisa la’akari da yadda mutane za su iya biyan kudin ruwan.