Hukumar YOSEMA ta raba kayan agaji ga wadanda ambaliya ta shafa
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA) ta rarraba kayan agaji da suka hada da kayan abinci da wadanda ba na abinci ba, ga mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a Jajimaji, hedikwatar karamar Hukumar Karasuwa. Kwanakin baya ne bala’in ya fada wa daruruwan magidanta, inda kwazarin ruwan sama ya ruguza musu […]
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA) ta rarraba kayan agaji da suka hada da kayan abinci da wadanda ba na abinci ba, ga mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a Jajimaji, hedikwatar karamar Hukumar Karasuwa. Kwanakin baya ne bala’in ya fada wa daruruwan magidanta, inda kwazarin ruwan sama ya ruguza musu gidaje. Kayan da aka raba sun hada da shinkafa da gero da dawa da man gyada da taliyar Indomi da barguna da bokitan roba da kuma sutura. Kamar yadda Shugaban karamar Hukumar Karasuwa, Alhaji Ubaliyo Gambo ya bayyana, karamar hukumar tana shirin sauya wa al’ummar da abin ya shafa wurin zama domin kauce wa sake fadawa cikin irin wannan bala’i a garin.