Hukumar zabe ta bankado sabuwar hanyar sayan kuri’a

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bankado da sabon shirin hanyar sayan kuri’ar masu zabe. Wannan shirin kuwa shi ne, ‘yan siyasa na amfani da masu sayar da abinci da ke zaune a harabar mazabar kada kuri’a, sakamakon cewa akwai adadin jama’a da suke tare da masu sayar da abincin wanda hakan […]

Hukumar zabe ta bankado sabuwar hanyar sayan kuri’a

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bankado da sabon shirin hanyar sayan kuri’ar masu zabe.

Wannan shirin kuwa shi ne, ‘yan siyasa na amfani da masu sayar da abinci da ke zaune a harabar mazabar kada kuri’a, sakamakon cewa akwai adadin jama’a da suke tare da masu sayar da abincin wanda hakan zai zama wata hanya mafi sauki ta sayan kuri’a da kudi.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne sanar da hakan jiya Abuja lokaci da ayarin Tarayyar Turai masu lura zabuka da mambobin kasashen Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS suka ziyarci hedkwatar INEC.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta