Hukumar zabe ta gano cibiyoyin ragista na bogi a Neja

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar Neja ta ce ta bankado cibiyoyin ragistar zabe na bogi a karamar hukumar Zungeru da Wushishi na jihar.   Shugaban hukumar zaben na jihar, Farfesa Sam Agwu ya fada wa Aminiya jiya a garin Mina cewa ’yan sanda ne suka yi wa cibiyar bogin dirar mikiya […]

Hukumar zabe ta gano cibiyoyin ragista na bogi a Neja

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar Neja ta ce ta bankado cibiyoyin ragistar zabe na bogi a karamar hukumar Zungeru da Wushishi na jihar.
 
Shugaban hukumar zaben na jihar, Farfesa Sam Agwu ya fada wa Aminiya jiya a garin Mina cewa ’yan sanda ne suka yi wa cibiyar bogin dirar mikiya bayan da suka samu bayanan sirri inda suka kama wanda ake zargi da dimbin katunan zabe.
 
Farfesa Egwu ya ce yawancin wadanda mutumin ya damfara ma’aikatan wani kamfanin gine-gine ne wadanda suka nemi katin zaben ko kuma wasu takardu da za su sanya a yi musu ragista a zabe mai zuwa.