Hukumar zabe: Tsumma makunshin cuta

Makasudin gudanar da zabe a dukkan kasashen duniya shi ne fahimtar ra’ayin jama’a game da dacewar ’yan takara don ba su damar darewa mukamai daban-daban da kuma ba jam’iyyun siyasar da suka yi nasara ikon kafa gwamnati. Amma al’amarin ba haka nan yake kasancewa ba a Najeriya, inda akwai hukumar zaben da ake cewa tana […]

Hukumar zabe: Tsumma makunshin cuta
Hukumar zabe: Tsumma makunshin cuta

Makasudin gudanar da zabe a dukkan kasashen duniya shi ne fahimtar ra’ayin jama’a game da dacewar ’yan takara don ba su damar darewa mukamai daban-daban da kuma ba jam’iyyun siyasar da suka yi nasara ikon kafa gwamnati. Amma al’amarin ba haka nan yake kasancewa ba a Najeriya, inda akwai hukumar zaben da ake cewa tana zaman kanta, amma duk da haka nan ba ta da ’yancin cin gashin kanta domin kuwa Shugaban kasa ne ke nada shugaba da kwamishinoninta, sa’anan kuma Majalisar Dattijai ta amince kafin hakan ya tabbata. Shugaban kasa kuma na da ikon korar shugaban hukumar ko wani daga cikin kwamishinonin hukumar zaben a duk lokacin da ya ga dama ba tare da waiwayar Majalisar Dattijan ba.
Wannan al’amari ya kasance tamkar dabaibayi ga hukumar da kuma ma’aikatanta domin kuwa hakan na bayar da dama a karkata ta yadda ake bukata, kuma cikin manyanta babu wanda ya isa ya ki amincewa da umurnin da aka ba shi don sakin hanya da karya ka’idojin gudanar da aikinsa. An sha yin kuka da hukumar zabe game da haka, an kuma dauki matakan yin gyararraki da yawa don fitar da hukumar daga cikin wannan mawuyacin yanayi don share kukan talakawa game da rashin ingancin aikinta, amma ba a kai ga nasara ba, hasali ma  lamarin kara dagulewa yake yi a dukkan lokutan da aka yi zabe.
Shi ya sa mutane ke ganin cewa matsololin da ke tayar da zaune tsaye da wadanda suke haddasa husuma da tarzoma da masu  sanya batutuwan bambancin kabilanci da na addini suna kara kamari a kasar nan, duk sun samo asali ne daga rashin ingancin hukumar zabe, wacce talakawa ke cewa da ita gara babu. Ya tabbata cewa ta kan hukumar zaben ne ake bi ana samar da shugabannin da ba su iya yin wani katabus bisa kan karagar mulki domin kuwa tun can da farko ba su ne suka fi dacewa da mulkin ba, a sakamakon haka nan kuma jama’a ba su ganin su da mutunci domin sai da suka sayar da mutuncinsu ga marasa mutunci, aka yi aikin rashin mutuncin, sannan su ma suka samu damar mike kafa kan kujerar tsabar rashin mutunci. To ta ina ke nan harkokin gudanar da mulki da kuma kyautata wa jama’a za su yi armashi tun da dai ba a dora su bisa ginshikin adalci  ba?
Duk da wayewar kan jama’ar Najeriya da kuma ci gaban da ake ta kwanzartawa a fannonin siyasa da mulki, har yanzu dai ita ce koma bayan sauran kasashe masu tasowa a duniya game da cin  gajiyar zabubbukan shugabanninsu, kuma hakan shi ke sa jama’arta na kasancewa asfala-safilin, watau kaskantattun mabiya tafarkin dimokuradiyyar da ba ta da wani alfanu a gare su. Kamar yadda ba a yin wasa ba tare da dariya ba, haka ne kuma ba a yin zabe son barka  a Najeriya, domin kuwa jama’a za su yi ta guna-guni game da sakamakonsa: wasu na Allah-Ya-isa, wasu na tsinuwa game da yadda aka gudanar da shi, wasu kuma na mugun alkaba’i game da bakin cikin da ya jefa dimbin jama’a a ciki. Har yanzu a Najeriya ba a yin zabe da ingantacciyar rajistar masu jefa kuri’a, ba a kuma samar da dukkan takardu da kayayyakin zabe a tashoshin jefa kuri’a, sai a kai wasu, a kuma bar muhimmai daga cikinsu, musamman ma na rubuta sakamakon zaben rumfuna. Wadannan sakacin suna jawo manyan laifuffukan da kowannensu na iya sa hukumar sauraron kararrakin zabe ta soke sakamako ko ma zaben dungurungum.
Abin takaici game da haka shi ne hukumar zabe ba ta koyi darasin komai ba game da haka, ba ta kuma sauya halayen da ke sa jama’a na dawowa daga rakiyarta ba a dukkan lokuta. Har yanzu tana zakewa a murdiyar zabe, kuma ba ta girmama zabin jama’a, sai biye son zuciyar iyayen gidanta wadanda ke rubuta mata sunayen ’yan takarar da za ta gabatar a matsayin masu nasara. A takaice dai ana iya cewa hukumar zaben ba ta daina aikata dukkan magudin da suka sha tafkawa tun daga zamanin Jamhuriya ta farko ba, ba ta kuma mance  dabarun munakisa da almundahana ba wajen tadiye dan takaran da ke da farin jinin jama’a, amma ba shi ne  hukuma ke so ba.
Abin takaici game da hukumar zaben Najeriya shi ne tana kara girma ne tana kuma ci gaba da wasa da kasa. Irin abubuwan da suka faru a makon jiya game da zaben Gwamnan Jihar Anambra sun nuna mana cewa har yanzu dai mahukuntan kasar nan na ci gaba da dora hukumar zabe bisa mummunan tafarkin da ke kai ta koyon saka da mugun zare ga shi a yanzu ta zama tsumma makunshin cuta, kuma illolin da suka biyo bayan haka za su ci gaba da wanzuwa har ya zuwa shekarar 2015 inda za a kwata kwatankwacin haka a daukacin tarayyar jamhuriyar Najeriya, kuma a lokacin ne talakawa za su yaba wa  aya zaki.