Hukumar zaben Malawi ta umarci kara kidaya kuri‘u

Hukumar zaben Malawi ta umarci kara kidaya kuri’un da aka kada a zaben kasar bayan samun kwararan hujjojin da suka tabbatar da kura-kurai a zaben, wanda hakan kuma ya jefa kasar cikin rudanin siyasa.Shugaban Hukumar Zaben Madon Mblendera , ya ce “ a lokacin da ake fara tattara kuri’u, an samu lokutan da yawan wadanda […]

Hukumar zaben Malawi ta umarci kara kidaya kuri‘u
Hukumar zaben Malawi ta umarci kara kidaya kuri‘u

Hukumar zaben Malawi ta umarci kara kidaya kuri’un da aka kada a zaben kasar bayan samun kwararan hujjojin da suka tabbatar da kura-kurai a zaben, wanda hakan kuma ya jefa kasar cikin rudanin siyasa.
Shugaban Hukumar Zaben Madon Mblendera , ya ce “ a lokacin da ake fara tattara kuri’u, an samu lokutan da yawan wadanda suka kada kuri’a ya fi na wadanda sunayensu yake cikin rijistar kada kuri’a. Mun cinma matsaya da jam’iyyun siyasa ta yadda za a gyara hakan, inda suka amince da mu kara kidaya kuri’un da hannu.  Kuma har mun yi nisa da aikin, amma ba za mu san tsawon lokacin da aikin zai kai mu ba”.
A ranar Asabar da ta gabata ne, Shugabar kasar Joyce Banda ta bayyana soke zaben bisa dalilan dimbin kura-kurai da kuma magudi da wasu suka zargin an yi a zaben. Ta kuma bukaci sake sabon zabe a cikin kwana 90 wanda ta ce ba za ta tsaya takara ba, amma jim kadan bayan sanarwar ne, Babbar Kotun kasar ta umarci hukumar zaben da ta ci gaba da tattara kuri’un kuma ta ce Misis Banda ba ta ikon dakatar da shi.