Hukumomin gwamnati sun gana a kan laifukan intanet

Mai ba Shugaban Kasa Shawara a Kan Harkokin Tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya),  ya yi ganawar sirri da shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati a kan matsalar aikata laifuffuka a intanet. Wata sanarwa da jami’i mai kula da dabarun sadarwa a Ofishin NSA, Zakari Usman, ya fitar da safiyar Talata, yayin ganawar an […]

Hukumomin gwamnati sun gana a kan laifukan intanet

Babagana Monguno, Mashawarcin Shugaban Kasar Najeriya kan Tsaro. (Hoto: NTA).

Mai ba Shugaban Kasa Shawara a Kan Harkokin Tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya),  ya yi ganawar sirri da shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati a kan matsalar aikata laifuffuka a intanet.

Wata sanarwa da jami’i mai kula da dabarun sadarwa a Ofishin NSA, Zakari Usman, ya fitar da safiyar Talata, yayin ganawar an tattauna a kan sababbin kalubalen da ke kunno kai a wannan bangaren.

Taron, wanda shi ne irinsa na bakwai, ya kuma tattauna hanyoyin sauƙaƙa da ƙarfafa matakan aiwatar da Manufor Hana Aikata Laififfuka a Intanet ta Kasa ta 2021.

Monguno, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Mashawarta a kan Laifuffukan Intanet, ya koka da yadda bata-gari masu amfani da intanet don aikata laifuffuka ke barnata muhimman na’urorin sadarwa na kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 23 ga watan Fabrairu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da Manufor Hana Aikata Laififfuka a Intanet ta Kasa.

Mai magana da yawun ofishin na NSA, Zakari Usman, ya bayyana cewa majalisar ta tattauna a kan hanyoyin ba da kariya ga muhimman na’urorin sadarwa na kasa.

Ya kara da cewa, “Ofishin Mai Ba Da Shawara ga Shugaban Kasa a Kan Harkar Tsaro ya yi wa majalisar Karin bayani a kan kare muhimman bayanan kasa kamar yadda aka ayyana a cikin dokar da ta haramta laifuffukan intanet ta shekarar 2015”.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos