Hukumomin Jamus sun kwace karen wanda ta gaza biyan haraji sun sayar

Wata kafar labarai ta kasar Jamus ta ruwaito cewa, an kwace karen wata mata saboda gaza biyan kudin haraji inda aka sanya karen a kasuwar Intanet ta eBay. Rahoton ya ce, hukumomin birnin Ahlen a Jamus da farko sun yi yunkurin kwace keken guragu ko marasa lafiya  na wani nakasasshe a gidan saboda keken na […]

Hukumomin Jamus sun kwace karen wanda ta gaza biyan haraji sun sayar

Karen da aka sa a kasuwar eBay

Wata kafar labarai ta kasar Jamus ta ruwaito cewa, an kwace karen wata mata saboda gaza biyan kudin haraji inda aka sanya karen a kasuwar Intanet ta eBay.

Rahoton ya ce, hukumomin birnin Ahlen a Jamus da farko sun yi yunkurin kwace keken guragu ko marasa lafiya  na wani nakasasshe a gidan saboda keken na da matukar muhimmanci a gare shi, fiye da sauran abubuwa a harabar gidan.

To amma maimakon su tafi da keken sai suka kwace karen gidan mai suna Edda. Daya Jami’an da suka kwace karen sun sa wa karen farashin Yuro 750 (daidai da Naira dubu 305 da 59 da kwabo 50) ga mai bukata ya biya don mallakar karen.

Jaridar Ahlener Tageblatt ce ta fara wallafa rahoton a matsayin tsakure daga rahoton.

An sayar da kare Edda ga Michaela Jordan, wadda  ’yar sanda ce. Kuma ta bayyana wa majiyar Ahlener Tageblatt cewa da farko ta yi wani tunani daban kasancewar yadda ta ji saukin farashin da aka sa wa karen da za a sayar. Hakan  ya sa ta kira lambar sadarwar masu tallata karen wadanda ma’aikatan hukuma ne a Ahlen sai wani ya fara yi wa Michaela Jordan bayanin cewa, asalin wanda ya mallaki karen hukumar birnin na bin sa kudi ne da suka hada da rashin biyan kudin harajin kare, hakan ya sa aka sa karen a kasuwa don biyan kudin harajin.

An yi wa Michaela Jordan bayanin cewa, karen yana cikin koshin lafiya don haka ta amince ta sayi karen.

Daga bisani bayan sayen Edda, Michaela Jordan ta gano cewa, karen bai da koshin lafiya kuma ba a sanar da haka ba kafin a sa shi a kasuwa. Sai daga baya ta samu rahoton cewa tun lokacin da aka samu musayar mallakar karen a watan Disamba an yi wa karen tiyata har sau hudu saboda matsalar ciwon ido da kuma wata tiyatar gaggawa da aka yi wa karen lokacin Kirsimeti.

Misis Michaela ta bukaci hukumomin su biya ta Yuro 1,800  (kimanin Naira dubu  731 da 932 da kwabo 20. A cewar rahoton bukatar Misis Michaela ta sayen karen ne janyo hankalin majiyar Ahlener Tageblatt ta wallafa cikakken rahoton, wanda hakan ya sa a aka bankado asalin wanda ya mallaki Edda.

Asalin wanda ya mallaki karen ya ce, wannan ba tsabtataccen ciniki ba ne, amma wadda ta sayi karen ta amince da sayen ne a kasuwar eBay.

Tun a farko dai jaridar Ahlener Tageblatt ta bayyana cewa, jami’an hukumar birnin sun shiga gidan wanda ya mallaki Edda ne da nufin daukar keken guragu sanadiyyar rashin biyan kudin haraji da ba su yi ba, daga bisani suka yanke shawarar tafiya da karen gidan don sayarwa a eBay da nufin biyan bashin kudin harajin da hukuma ke bi.

 

 

 

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas