Hukumomin sufurin jiragen ruwa sun kudiri aniyar aiki tare

Shugabanin sufurin jiragen ruwa sun yi alkawarin aiki tare da tuntubar juna akai-akai domin habaka bangaren da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa.  A taronsu na wata-wata da ya gudana a ranar Talatar,  sun jadadda muhimmancin aiki tare da hadin gwiwa da bangaren sufurin jiragen kasa domin bunkasa shi. Babban Daraktan Hukumar kula da Lafiyar  Teku […]

Hukumomin sufurin jiragen ruwa sun kudiri aniyar aiki tare

Shugabanin sufurin jiragen ruwa sun yi alkawarin aiki tare da tuntubar juna akai-akai domin habaka bangaren da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa. 

A taronsu na wata-wata da ya gudana a ranar Talatar,  sun jadadda muhimmancin aiki tare da hadin gwiwa da bangaren sufurin jiragen kasa domin bunkasa shi.

Babban Daraktan Hukumar kula da Lafiyar  Teku da Sufurin Jiragen ruwa ta kasa  (NIMASA) Bashir Yusuf Jamo ya shaida wa Aminiya cewa, manyan masu ruwa da tsakin sun cimma matsayar yin hada kai tare da aiki tukuru domin ciyar da ɓangaren gaba.

Ya ce sufurin jiragen ruwa, na da muhimmanci a tarihin sufuri na duniya.

“Shi ya sa ko da aka dakatar da nau’ikan sufuri a sassan duniya saboda annobar coronavirus, ba a dakatar da sufurin jiragen ruwa ba, saboda tasirinsa da muhimmancinsa, don haka cigaban sashen cigaba ne na kasa baki daya”, inji shi.

Bashir Jamo ya ce hadin gwiwar da aka samu tsakanin shugabanin sufurin jiragen ruwa, dama ce ta magance matsaloli da suka dade suna addabar bangaren.

Don haka suka hadu da shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), Hadiza Bala, da Hukumar kula da Kogunan da suka Ratsa  Jihohi (NIWA), da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo sauyi”, inji shi.

A nata bangaren shugabar NPA Hadiza Bala ta jadadda mahimmancin aiki tare da sauran bangarorin sufurin kasa domin bunkasar sufuri a Najeriya.

Hakazalika Babban sakataren Hukumar Jiragen Ruwa ta kasa (NSC) Hassan Bello ya shaida wa Aminiya cewa hadewar da suka yi zai kawo bunkasar tattalin arzikin kasa.

“Sashen sufuri bangare ne da kasar nan za ta iya mora ta fuskar samar da kudin shiga maimakon dogaro da bangaren albarkatun man fetur”, inji shi.