Hukunce-hukuncen Layya da Sallah Babba

Mutane za su iya haɗa kuɗi su sayi dabbar layya guda ɗaya su yanka. Amma dole sai idan sa ne ko raƙumi za su yanka, kuma masu haɗa kuɗin ba su wuce mutum bakwai ba

Hukunce-hukuncen Layya da Sallah Babba

Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Honorabul Femi Gbajabiamila yana yanka ragon layyarsa ranar Sallah (Hoto: Ofishin Yada Labarai na Shugaban Majalisar Wakilai)

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana ranar Litinin 18 ga Mayu 2026 ta zama ɗaya ga watan Zul-Hajji 1447 Bayan Hijira.

Sanarwar da Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanya wa hannu ta ƙara da ranar Talata mai zuwa ce za ta zama ranar Arafa, Laraba kuma za ta kasance ranar Babbar Sallah.

A watan Zul-Hajji, ana buƙatar Musulmi su yi azumin nafila, tare da yawaita ayyukan ibada da zikiri, tun daga ranar farko har zuwa 9 ga wata, sannan a yi irin Babbar Sallah a ranar 10 ga wata.

Azumin 9 ga watan Zul-Hajji, wato ranar Arafa, ya keɓanata ga wanda bai samu zuwa aikin Hajji ba, kuma yana da falala mai tarin yawa.

Waɗanda za su yi Layya kuma ana buƙatar su guji aske kowane irin gashi daga jikinsu ko yanke farce ko cire wani abu daga jikinsu har sai bayan sun yanka da bar layyarsu.

A ranar 10 ga wata, ana buƙatar Musulmi su kama baki, kar su ci komai ha sai an sauko daga sallar idi.

Haka kuma ana so Musulmi su ci gaba da yin kabbara a duk bayan Sallar farilla, daga bayan Sallar Asuba ta safiyar Babbar Sallah har zuwa bayan La’asar na ranar 13 ga watan Zul-Hajji.

A ranar Sallah, ana so mutum ya yi wankan ibada, ya sanya turare ya sa sababbin tufafi, ko mafi kyawun tufafinsa, ya yi ado, sannan ya fita zuwa masallaci ko filin idi.

Ana so kowa ya fita zuwa sallar idi, maza da mata da ƙananan yara da tsofaffi, kai har da mata masu jinin al’ada. Sai dai su mata masu jini, za su koma dafa gefe.

Amma duk da haka ba a son mata su bayyana adonsu, ko su fita sanye da tufafi masu bayyana surar jikinsu, so kuma turare mai jan hankali, ko riƙa caƙuduwa tsakanin maza da mata.

A filin idi zama ake yi kawai, ba a yin sallar nafila. Idan liman ya zo sai a yi Sallar Idi, daga nan sai ya gabatar da huɗuba, bayan nan kuma ya yanka dabbar layyarsa, idan akwai.

Ga wanda zai yi Layya kuma, wajibi ne ya jira sai bayan an sauko daga sallar idi kuma limamin garin da yake ya yanka dabbar layyarsa, kafin shi ya yanka tasa.

Idan liman ba shi da abin yin layya kuma, da zarar ya kammala huɗuba, zai ba da izini mutane su yanka abin layyarsu.

Kuma an fi so duk wanda ya yi Layya, to abin da za su fara ci a ranar ya kasance daga naman layyarsa.

Ana ci gaba da yanka dabbobin layya har zuwa kafin faɗuwar rana. Ya halatta a yanka abin layya daga ranar Babbar Sallah zuwa ranaku uku bayan nan, daga hatsi zuwa faɗuwar rana.

Amma a tuna a ranar farko, dole sai bayan saukowa daga sallar idi, idan limamin garin ya yanka nasa ko ya ba da izini ga jama’a su yanka nasu.

Ana yin layya ne da nau’in dabbobi huɗu kawai, wato tumaki (rago da tunkiya) ko awaki (akuya da bunsuru) ko rakuma (amale da raguwa) ko shanu (maraki da saniya).

Idan akuya ce ko bunsuru, dole sai  sun kai wata shida zuwa sama za a iya yin layya da su, amma tumaki sai daga shekara zuwa sama. Shanu kuma daga shekara biyu zuwa sama. Raƙuma kuma dole sai mai biyar zuwa sama.

Idan da shanu ko raƙumi za a yi layya, mutane za su iya haɗa kuɗi su yi da dabba ɗaya, amma ba su wuce mutum bakwai. Amma a tuna, sai idan da dangin raƙuma ko shanu za a yi.

Sannan ana so dabbar layya ta kasance mai ƙoshin lafiya, kuma wadda ba ta da wata tawaya, kamar ido ɗaya ko gurgunta ko wadda take fama da wani ciwo ko karaya wanda bai warke ba.

Mace tana iya yin layya, haka ma mara aure, matuƙar suna da hali, ba sai magidanci kawai ko namiji ba. Magidanci kuma zai iya sanya iyalansa a cikin layyarsa.

Yadda ake so mutum ya sarrafa naman layyarsa shi ne, shi da iyalinsa su yi amfani da wani kashi, ya yi sadaka da wani kaso, sannan ya raba wa maƙwabtansa mabuƙata wani kaso.

Muhimmin abin da ya kamata a sani shi ne, yin lau6ya Sunna ce wajiba ga duk wanda ke da hali, namiji ne ko mace, magidanci ko mara aure.

Babban abin da ake buƙata ga mai yin lauya shi ne ya tsarkake niyyarsa, da cewa zai yi ne domin neman yardar Allah da samun lada, ba don kece raini ba ko riya.