Hukunce-Hukuncen sakin aure a Musulunci
Kuma Yana bayyana ayoyinSa ga mutane don su wa’azantu.
Musulunci addini ne da ya kunshi komai da komai don inganta rayuwar dan Adam a duniya da Lahira.
Bai bar dan Adam ya yi amfani da hankali da tunaninsa kawai don tsara wa kansa makoma ba, saboda shi dan Adam mai rauni ne, mai son zuciya ne, mai hadama ne, mai rowa ne, kai karewa ma mai butulci ne ga wanda Ya halicce shi.
- Ba da tazarar haihuwa Musulunci ya amince a yi ba kayyade iyali ba — Jabir Maihula
- Mene ne bambancin ’yan siyasa da ’yan ta’adda?
To in har zai yi butulci ga Mahaliccinsa, ta yaya zai tsara rayuwar da sauran abokan zamansa za su ji dadi?
Aure daya ne daga cikin ginshikan rayuwar al’umma, wannan ya sa Musulunci bai bar shi sasakai ba ka’idoji da dokoki ba. Kuma baya ga ka’idojin zamantakewa a tsakanin ma’auratan, duk da ba a fata, amma ya tsara yadda za a rabu idan aka kasa samun jituwa ko maslaha a tsakanin miji da matar.
A cikin Alkur’ani Mai girma a Suratul Bakara Aya ta 221. Allah Madaukaki Yana cewa: “Kuma kada ku auri mushrikai mata (arna), har sai sun ba da gaskiya. Hakika baiwa mumina ta fi mushrika koda ta kayatar da ku.
“Kuma kada ku aurar wa mushrikai maza wadanda kuke yi wa walicci, har sai sun ba da gaskiya.
“Hakika bawa mumini ya fi kafiri, koda (kafirin) ya kayatar da ku.
“Wadancan suna kira ne zuwa ga wuta, Allah kuma Yana kira ne zuwa ga Aljanna da gafara da izininSa.
“Kuma Yana bayyana ayoyinSa ga mutane don su wa’azantu.”
222. “Kuma Suna tambayarka game da haila. Ka ce da su, “Ita haila cuta ce saboda haka sai ku nisanci mata a cikin haila.
“Kada ku kusance su har sai sun yi tsarki, sannan idan sun yi wanka sai ku zaike musu ta yadda Allah Ya umarce ku.
“Hakika Allah Yana son masu tuba kuma Yana son masu tsarki.”
Sharhi: Yahudawa sun kasance suna matsawa sosai game da haila, suna kyamar matansu idan suna haila, suna gudunsu har ma wajen barci da wurin cin abinci da wurin shaye-shaye.
Amma a nan Allah Ya ba da amsa ne game da tambayar da aka yi game da haila da cewa Musulmi su nisanci jima’ai da matansu, idan suna haila har sai sun yi tsarki, amma duk sauran abubuwa sun halatta su yi da su.
223. “Matanku gonakinku ne, sai ku zo wa gonakinku ta inda kuka so, kuma ku gabatar da (basmala da hamdala da addu’o’i na alheri) don kanku, ku ji tsoron Allah, ku sani hakika ku masu gamuwa da Shi ne.
“Kuma ka yi wa muminai albishir “dakyakkyawan sakamako).”
Sharhi: A wannan ayar Allah Yana yi wa mutane hannunka mai sanda ne game da matan da suke aure cewa su kula da su kamar yadda suke kula da gonakinsu, domin daga gare su ne za su samu zuriya wadanda su ma lallai ne su kula da yi musu kyakkyawar tarbiyya.
Idan ko ba haka ba, to, za su tashi su girma cikin mummunan hali na lalacewa ko su fada kafirci in ba a yi sa’a ba, kamar yadda amfanin gona zai lalace idan bai samu kyakkyawar kula ba.
Hadisin Annabi (SAW) da Buhari ya ruwaito ya ce, “Dukkan abin haihuwa an haife shi ne a kan tafarkin Musulunci, sai dai iyayensa su mayar da shi Bayahude ko Banasare ko Bamaguje.”
Ashe wajibi ne kowane uba ya yi wa da ko ’yarsa tarbiyya ta Musulunci domin yarayu Musulmi kamar yadda Allah Ya halicce shi Musulmi. Yin haka shi ne amsa wannan kira da Allah Ya yi.
224. “Kada ku sanya rantsuwa da Allah ta zama kariyar (don kin) yin aikin alheri ko yin takawa ko yin sulhu a tsakanin mutane.
“Allah Mai ji ne, Masanin abin da kuka fada ko kuka aikata.”
Sharhi: Idan mutum ya rantse kan zai yi wani abu ko ba zai yi ba. Sai wannan rantsuwar ta hana shi aikata alheri, to a nan dole ne ya karya rantsuwarsa domin ya aikata alherin ko ya fasa yin sharri.
An samo a cikin Hadisi cewa, duk wanda ya yi rantsuwa a kan wani abu sai ya ga wani abu sabanin wanda ya yi rantsuwa a kai ya fi masa alheri, to sai ya dauki wanda ya fi masa, ya karya rantsuwarsa ya yi kaffara.
225. “Allah ba Ya kama ku da kuskure a cikin rantserantsenku, amma yana kama ku da abin da zukatanku suka kudurce. Kuma Allah Mai gafara ne Mai hakuri.”
Sharhi: Allah ba zai kama ku ba kan rantsuwar da kuka yi ba da sani ba a cikin hirarku, don haka ba zai yi muku azaba ba a kan haka, kuma ba za ku yi kaffara ba saboda ita.
226. “Dakatawar wata hudu ta tabbata ga wadanda suke yin rantsuwar ba za su kusanci matansu ba, sannan idan sun komo wurin matansu, to hakika Allah Mai gafara ne Mai jinkai a gare su.”
Sharhi: A nan Allah Yana tsara irin yadda za a warware wasu abubuwa da suke faruwa ne da wasu mutane cikin harkokin aure da kuma tsakanin miji da mata.
Idan wani abu ya faru a tsakaninsu da matansu, sai suka rantse cewa ba za su sake kusantarsu ba sai wani lokaci, ko kuma suka rabu da su ba tare da kayyade lokaci ba, wato su bar su a rataye kamar jemage, su ba su kula su ba, kuma su ba su sake su ba, to, irin wannan yana sa mata su galabaita kwarai.
To idan wannan ya faru wato ya rantse ba zai kula matarsa ba, bai kuma kayyade wani lokaci ba, to lallai ne a kansa ya zabi daya daga cikin abubuwa biyu kafin wata hudu, wato ya sadu da ita ko kuma ya sake ta.
Bai halatta ba ya wuce wata hudu, idan ya komo wa matarsa a cikin wata hudun na shi ke nan sai su ci gaba da aurensu, amma kuma wajibi ne a kansa ya yi kaffara saboda rantsuwar da ya yi.
Idan kuma bai kula matar ba har bayan wata hudu, to tana iya kai kararsa ga alkali ko wani hakimi ya raba aurensu.
SP Ahmad Adam Kutubi (PhD) Zone 7 Police Headkuaters Wuse Zone 3, Abuja 08036095723, 07045472372