Hukuncin da ake yanke wa ‘yan Boko Haram da aka kama ya yi daidai?

Hukuncin da aka yi masu ya yi kaxan – Sa’adatu Muhammad Ka’oje Daga Nasiru Bello a Sakkwato  Sa’adatu Muhammad Ka’oje: “Hukuncin da aka yi masu bai dace ba don kowa yasan abin da suka yi a qasar nan na kashe mutane da cin zarafin mata da wulaqanta yara sananan ace sun qare ne a xaura […]

Hukuncin da ake yanke wa ‘yan Boko Haram da aka kama ya yi daidai?

Hukuncin da aka yi masu ya yi kaxan – Sa’adatu Muhammad Ka’oje

Daga Nasiru Bello a Sakkwato 

Sa’adatu Muhammad Ka’oje: “Hukuncin da aka yi masu bai dace ba don kowa yasan abin da suka yi a qasar nan na kashe mutane da cin zarafin mata da wulaqanta yara sananan ace sun qare ne a xaura kawai, kuma su gama su fito sun ci bilis ke nan. Bana tare da wannan hukunci. A matsayina na mace na san irin wahalar da mata ‘yan uwana ke sha a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Borno da Yobe da sauran wurare a qasar nan, kuma duk sanadin waxannan mayaqan. Zawarawa sun qara yawa don an kashe mazansu, an keta haddin mata da budurcinsu, ta yaya zan goyi bayan a bar mai son kashe wasu da kassara su. Ya kamata gwamnati ta sake duba hukuncin da za ta yi masu. Don samun maslaha da xorewar zaman lafiya a riqa hukunci duk abin da ka yi a yi maka.”

Hukuncin ya yi daidai na goyi bayan yadda aka yi – Abubakar Abdullahi Kajiji

Daga Nasiru Bello a Sakkwato 

Abubakar Abdullahi Kajiji: “Hukuncin da aka yankewa ‘yan Boko Haram ya yi daidai kuma na goyi bayan yadda aka yi, sannan kuma haka ya nuna shari’a a qasar nan tana aiki, kuma hakan zai iya zama darasi ga ‘yan qungiyar ta Boko Haram su iya shiga taitayinsu, su fahimci wannan ba hanya ce da za ta vulle masu ba sai wahala da rashin kwanciyar hankali da guje-guje, kuma in sun shiga hannu ayi masu hukunci. Wahala saman wahala. Yi musu shari’a abu ne da zai ci gaba da karya lagonsu, in har ma ba a qarar da su ba, ballantana ma an xauko hanya.”

Ba kamar yadda aka so ba – Alhaji Hayatuddin Muhammad

Adam Umar, Abuja

Alhaji Hayatuddin Muhammad: “Gurfanar da su a gaban shari’a ya yi, sai dai ba kamar yadda a ka so ba. Dalilina kuwa shi ne ire-iren waxanda su ka ce ba su yi nadamar abin da su ka aikata ba sannan har su ka yi iqirarin za su sake aikata hakan idan su ka samu dama, ban ga dalilin ci gaba da tsaresu ba illa a zartar masu da hukuncin kisa a kansu kamar yadda su ka yi wa wasu a baya. Saboda ci gaba da tsaresu ko da na shekara nawa ne bai da wani amfani sai ma ya basu damar gurvata qwaqwalen wasu da aka tsaresu tare. Sai kuma waxanda a ka samu ba su da laifi a ka sallamesu, kamata ya yi gwamnati ta biyasu diyya gwargwadon adadin shekaru da su ka yi su na tsare wata qila hadda uquba iri-iri.”

A musu hukuncin da ya dace da su – Bashir Muhammad

Adam Umar, Abuja

Bashir Muhammad: “Batun yi masu shari’a da kuma tsaresu hakanan ba tare da shari’ar ba ba zai tava zama xaya ba. Saboda ko ba komai a dalilin gurfanar da su a gaban shari’a, an ji ta bakinsu sannan aka yanke masu hukunci gwargwadon bayanansu da kuma abin da a ka gano. Sannan wasu da dama daga cikinsu kwasarsu aka yi aka saka su cikin wannan bala’in ba don su na so ba. Wasunsu kuma sun samu kansu ne a ciki bayan an gurvata masu qwaqwale. Ka ga ke nan duk su na da damar yi wa kotu bayani sannan ita kotun ta yi amfani da basirarta da kuma tsarin da dokar qasa ya bata, ta zantar masu da hukuncin da ya dace da su.” 

Ya kamata a gudanar da bincike sosai kafin a yanke hukunci – Mansur Khalid

Isiyaku Muhammed

Mansur Khalid: “Ni idai a nawa ra’ayin ya kamata a yi bincike, in har an tabbatar ‘yan Boko Haram ne sai kawai a kasha su. Idan kuma gidan yari za a kaisu, to ya kasance an musu xaurin rai da rai ne. Saboda idan kawai za a kaisu gidan yarin ne, watarana za a sake su dawo su ci gaba daga inda suka tsaya, ke nan kamar an kashe maciji ke nan ba a sare mai kai be.” 

Hukuncin bai yi ba – Bello Sagir

Isiyaku Muhammed

Sagir Bello: “A gaskiya hukuncin ni dai a ra’ayi na bai yi ba. Duk da an ce sharia sabanin hankali ce. Mene ne zai hana a yanke musu hukuncin kisa tunda da dai ai hakan ma bai savawa doka ba? Matsalar yanke musu hukuncin xauri ita ce, zai yiwu za su iya samu wata dama nan gaba, watakila ma nan kusa za su iya kuvuta daga gidan yarin. To ke nan mene ne amfanin xaurin tunda za su iya fitowa tun kafin ma wa’adin su ya kai rabi ko kuma ya qare?