Hukuncin da muka zartar na korar Gwamnan Kano na nan daram – Kotu
Kotun ta ce matsalar da aka samu tuntuɓen alƙalami ce, kuma za ta gyará
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yi ƙarin haske a kan ce-ce-ku-cen da ake yi kan kundin hukuncin da ta zartar da ya kori Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga kujerarsa a ranar Juma’a.
Kotun dai a hukuncinta na ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yi na soke nasarar Abba na jam’iyyar NNPP tare da maye gurbinsa da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.
- Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 25 a Neja
- Magoya bayan NNPP sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a Kano
Sai dai kwafin kundin hukuncin da ya bayyana ranar Talata na cike da ruɗani kuma ya janyo ce-ce-ku-ce matuka.
To sai dai da yake ƙarin haske a kan ka-ce-na-cen, Babban Magatakardar kotun, Umar Mohammed Bangari, ya ce abin da ya jawo matsalar tuntuɓen alkalami ne.
Ya kuma ce hakan ba zai canza hukuncin da alkalai suka sanar da murya ɗaya ba, wanda ya tabbatar da matsayin kotun ta baya.
Umar Bangari ya kuma ce za a gyara kuskuren da zarar ɓangarorin da shari’ar ta shafa suka bukaci yin hakan a rubuce.
Bugu da kari, ya jaddada cewa doka ta hudu a ɗaftari na 23 na kotun ta ba su damar yin gyara a kan duk wani tuntuben alkalamin da suka ankare ko kuma ɗaya daga cikin bangarorin da suke ƙara suka ankarar da su.
Ya ce saɓanin kururuwar da ake yi a kafafen sada zumunta, har yanzu soke nasarar Abban da suka yi tana nan daram.
Ya ce, “Abin da ya faru a wani ɓangare na hukuncin wani tuntuɓen alkalami ne da bai kamata ya jawo wani ka-ce-na-ce ba.
“Kotun na da damar gyara duk wani kuskure da aka lura da shi. Kuka za mu yi hakan a kan lokaci,” in ju Umar Bangari.
A wani labarin kuma, tuni Gwamna Abba ya garzaya Kotun Koli inda yake neman ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan guda biyu.