Hukuncin daurin rai-da-rai zai tabbata kan masu fyade a Nasarawa
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, ta amince da kudirin dokar haramta duk wani nau’i na cin zarafin mutane tare da samar da cikakkiyar kariya da tabbataccen tsari na kwato hakkin wadanda aka zalunta ta hanyar keta haddi. Sabon kudirin da majalisar ta shigar cikin doka ya tanadi cewa wadanda suka aikata laifin fyade za su fuskanci […]
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, ta amince da kudirin dokar haramta duk wani nau’i na cin zarafin mutane tare da samar da cikakkiyar kariya da tabbataccen tsari na kwato hakkin wadanda aka zalunta ta hanyar keta haddi.
Sabon kudirin da majalisar ta shigar cikin doka ya tanadi cewa wadanda suka aikata laifin fyade za su fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai don ya zama abin daukan izina ga sauran al’umma wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
- An kara lokacin rajisatar lambar dan kasa da layin waya
- COVID-19: Gwamnatin Taraba ta yi gargadi kan bukukuwa
Yayin zaman Majalisar da ke birnin Lafia da aka gudanar a yau Litinin, Ibrahim Balarabe Abdullahi, Kakakin Majalisar wanda ya dauki nauyin gabatar da kudirin shi ne ya sanar da bai wa kudirin gindin zama a dokokin jihar.
Kakakin Majalisar ya ce dokar ta tanadi hukuncin cin sarka na tsawon shekaru 14 ga duk wanda ya aikata laifin fyade da bai wuce shekaru 14 a duniya ba.
Aminiya ta ruwaito cewa a watan Satumban da ya gabata ne Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar zartar da hukuncin dandaka kan masu aikata fyade a jihar.
Kazalika, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ta Kaduna ya rattaba hannu kan dokar hukuncin mai tsanani a kan duk wanda a ka kama da laifin fyade.
Dokar ta ba da damar kisa ko dandanke ’ya’yan marainan duk wanda a ka kama ya yi wa kananan yara ’yan kasa da shekaru 14 fyade.
Haka kuma, karkashin dokar za a iya yanke musu hukuncin daurin rai-da-rai, kuma inda a ka kama mace dokar ta ce za a yanke mata wani sashe na al’aura ko kuma a kashe ta.