Hukuncin hana dalibai sanya Hijabi tauye ’yancin addini ne —MPAC

MPAC ta kuma yi kira ga kungiyoyin Musulmi da sauran masu kishin gaskiya da su yi magana kan wannan hukunci da ta kira “barazana ga ’yancin addini.”

Hukuncin hana dalibai sanya Hijabi tauye ’yancin addini ne —MPAC

Cibiyar Kare Muradun Musulmi (MPAC) ta bayyana rashin jin dadi da kuma kin amincewa da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ke Ibadan, ta yi na soke hukuncin Kotun Jihar Oyo da ya amince wa dalibai mata Musulmai 11 na Makarantar International School, Ibadan (ISI), da su rika sanya hijabi a matsayin wani ɓangare na kayan makaranta.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a, 3 ga Yuli, 2026, MPAC ta ce hukuncin ba wai batun rigimar kayan makaranta ba ne kawai, kutse ne ga ’yancin addini da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Rikicin sanya hijabin ya fara ne tun 2018, lokacin da ISI ta haramta wa dalibai mata Musulmai sanya hijabi.

Dalibai 11 tare da goyon bayan MURIC suka garzaya kotu, inda a ranar 22 ga Mayu, 2024, Alkalin Kotun Jihar Oyo, Mai Shari’a Moshood Ishola, ya yanke hukunci da ya ba wa daliban gaskiya, da cewa hana su sanya hijabi ya tauye musu hakkin addini.

Sai dai a ranar Juma’a 3 ga Yuli, 2026, Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin, inda ta ce makarantar ISI makaranta ce mai zaman kanta saboda ba ta karɓar tallafin gwamnati.

Alkalai biyu—Biobele Georgewill da K.I. Amadi—daga cikin uku sun goyi bayan soke hukuncin, da cewa hukuncin kotun koli kan sanya hijabi ya takaita ne ga makarantun da ke samun tallafin gwamnati.

A cewarsu, da cewa daliban sun “yi watsi” da ’yancin addininsu bayan sun rattaba hannu kan dokokin makarantar.

Sai dai Mai Shari’a Fadawu Umar ya yi adawa da wannan hukunci, inda ya ce daliban na da cikakken ’yancin sanya hijabi, hasali ma, babu dalilin daukaka karar.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa kulle daliban a dakin karatu na tsawon sa’o’i uku zuwa hudu ya sabawa ’yancinsu, sai dai ta rage diyyar da za a ba su daga miliyan daya zuwa dubu 200.

Matsayar MPAC

MPAC ta ce hukuncin ya saba wa kundin tsarin mulki, musamman Sashe na 38, wanda ya tanadi ’yancin yin addini da bayyana shi.

Ta yi gargadin cewa wannan hukunci zai iya zama hanyar ba makarantu masu zaman kansu damar tauye ’yancin dalibai Musulmi.

Cibiyar ta kuma yi kira g Kotun Daukaka Kara da ta amince da bukatar MURIC na dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an kai ga Kotun Koli.

Ta kuma roki Majalisar Dokoki ta Kasa da ta kafa doka da za ta tabbatar da ’yancin sanya hijabi a duk makarantu, ko na gwamnati ko na masu zaman kansu.

Kazalika ta bukaci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da ta fitar da ka’idoji da za su hana kowace makaranta tauye ’yancin dalibai bisa addini.

MPAC ta kuma yi kira ga kungiyoyin Musulmi da sauran masu kishin gaskiya da su yi magana kan wannan hukunci da ta kira “barazana ga ’yancin addini.”

A cewar MPAC, “’Yancin addini ba wani gata ba ne da za a ware bisa tsarin mallakar makaranta, kuma ba wani abu ba ne da yaro zai iya yin watsi da shi saboda shiga makaranta.”