Hukuncin kisa kan ’yan uwa Musulmi

Hukuncin kisa ga magoya bayan kungiyar ‘yan uwa Musulmi da wata kotu a kasar Masar ta yi da kuma daure hambararren Shugaba Muhammad Morsi na shekara 20 a gidan kaso. Hukuncin ya yi tsauri matuka musamman ganin cewa siyasa ce ta taka rawa muraran a wannan shari’ar. Kira ga Hukumar Zabe Hukumar Zaben Najeriya kallo […]

Hukuncin kisa kan ’yan uwa Musulmi
Hukuncin kisa kan ’yan uwa Musulmi

Hukuncin kisa ga magoya bayan kungiyar ‘yan uwa Musulmi da wata kotu a kasar Masar ta yi da kuma daure hambararren Shugaba Muhammad Morsi na shekara 20 a gidan kaso. Hukuncin ya yi tsauri matuka musamman ganin cewa siyasa ce ta taka rawa muraran a wannan shari’ar.

Kira ga Hukumar Zabe
Hukumar Zaben Najeriya kallo ya koma kanki domin al’ummar kasa sun amsa kira munyi zaben da muke ganin zai cire mana kitse daga wuta, Allah Ya sa ku bayyanawa al’ummar Jihar Taraba abin da suka zaba a gobe (Asabar) inda za a sake watan da kuka tsaida musu dan sake zabe a wasu wuraren.
Daga Hafizu Balarabe Gusau, 07035304499.

Kira ga ’yan ci-ranin da ke ketarawa Turai
Hakika yadda wasu ’yan uwanmu ’yan kasashen Afirka suke rasa rayukansu akan hanyar su ta zuwa cirani a wasu kasashen nahiyar Turai. Hakan abin damuwa ne da jimami da kuma takaici. Kuma babban kalubale ne ga shugabannin Afirka. Domin hakan bai rasa nasaba da yadda
’yan Afirkan ke dandana kudar su daga hannun shugabannin nasu. Ina fatan shugabannin za su gyara yadda suke tafiyar da mulki. Su inganta rayuwar al’ummominsu, domin su daina zuwa yawan ci-rani, inda har suke rasa rayukan su.
Daga Haruna Muhammad Katsina. Shugaban, 07039205659

’Yan matan Chibok: Gwamnati ta gaza
Assalamu alaikum, kowa ya yi da kyau zai ga da kyau a kwana a tashi asarar mai rai, ku ba ni dama na yi tsokaci game da sace ‘yan matan Chibok, da aka yi har tsawon shekara da wasu kwanaki, amma har ila yau babu duriyarsu. Abin bacin rai da takaicin shi ne gwamnatin PDP ta gaza ceto su daga hannun wadanda suka sace su, kana ta kwashe wadanda suka kubutan zuwa kasashen Amurka, da Ingila wai da sunan sanya su a makarantu domin ci gaba da karatunsu. Amma sannu a hankali bincike ya nuna cewa ‘ya’yan
masu hannu da shuni ne aka kaisu karatun, ba daliban mkarantar garin Chibok.
Ranar da aka yi juyayin tuna wa da ‘yan matan ne a garin Chibok wani mahaifiya shaida wa manema labarai cewa anyi amfani da sunan ‘ya’yansu ne aka fidda ‘ya’yan wasu karatu zuwa kasashen ketare, amma ba ‘ya’yansu ba.
Domin kuwa galibin ‘yan matan Chibok sunanan wasu a garin Yola wasu kuma a Babban Birnin Tarayya Abuja. Haba jama’a wane irin shugabanci ne ake gwada mana a Najeriya?
Sanin kowa ne hakkin shugaba ne ya kare rayuka, tare da dukiyoyin al’ummar da Allah Ya danka masa amanarsu, amma mu a Najeriya gwamnati ta gaza. Shugaba Goodluck Jonathan ya kamata ka kwana da sanin cewa duk wani abin
da ya faru da al’ummar Najeriya walau najin dadine ko kuma akasin haka to shi ne sila, kuma ranar gobe kiyama za kayi bayani a gaban sarki Allah. Don haka ka kagaggauta ceto ‘yan matan Chibok, dama sauran wadanda aka yi garkuwa da su a zamanin mulkinka kafin ranar 29
ga watan Mayu.
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Jihar Barno, 08032135939.

Kan siyasar Jihar Kebbi
Zuwa ga Edita, yanzu kan an buga ta kare a zaben gwamnoni da aka yi. Wasu talakawansu na sonsu, amma guguwar canji ta kaudasu wasu daman an gaji da su kamar mu nan Jihar Kebbi. Gilibin ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati da talakawa sun gaji da mulkin Gwamna Saidu dakingari, ganin irin yadda yake kauda kai daga wasu bukatun mutanen jihar yakamata duk yadda ake aga ’yan kasuwa na samun wani taimako daga wajen gwamnati. Kuma ma’aikata na samun hakkinsu daga wajen gwamnati, amma munan Jihar Kebbi mun kasa samun wannan jin dadi daga wajen Gwamna dakingari. Ya zo ya same mu kan mu hade, amma da zuwansa sai ya raba kawunan mu ya mayar da wasu ’yan mowa wasu ’yan bora sannan sai mu kwashe kwana 15 gwamna baya cikin Jihar Kebbi kuma da zarar ya dawo baya wuce kwana uku ya koma to ga sakamakon abin da ka shuka nan ka kwasa suma wadanda suka kawo ka, ka dinga yi musu wulakanci domin kawai samun wajen zama. Daga karshe yakamata mu yi wa sabon Gwamnan Sanata Atiku Bagudu fatan Allah Ya ba shi ikon yin mulki cikin adalci.
Daga Usman Adamu Aliero Jihar Kebbi, 07061594299