Hukuncin Kotu: Zaɓin da ya rage wa Abba Gida-Gida
A shekarar 2019, da kyar Ganduje ya tsallake tarkon da madugun ya dana masa.
Bayan Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar Kano ta soke nasarar Gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf tare da bayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan, yanzu abin da ya rage wa Gwamna Abba GidaGida, shi ne ya yi amfani da lokacin da doka ta ba shi wajen daukaka kara zuwa kotunan gaba.
Kotun ta soke ƙuri’a dubu 165 da 663 tare da umartar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta janye shaidar nasarar da ta miƙa wa Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ta mika wa Gawuna.
- Yadda aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna ke tafiyar hawainiya
- Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano biliyan 30 saboda rusau a Filin Idi
Alkalan kotun a karkashin jagorancin Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, sun soke kuri’un ne bisa hujjar cewa ba su da sitamfin INEC a jikinsu, wanda hakan ya saba wa dokar zabe, don haka ba halattattun kuri’u ba ne.
Tuni dai Jam’iyyar NNPP ta yi fatali da hukuncin sannan ta sha alwashin ɗaukaka kara.
Da farko dai Hukumar INEC ta ce Abba ya lashe zaben ne da ratar kuri’a miliyan 1 da dubu 19 da 602, inda Nasiru Gawuna ya samu kuri’a dubu 890 da 705.
A yanzu da kotun ta soke kuri’a dubu 165 da 663 daga cikin na Abba Kabir Yusuf sun zama kuri’a dubu 853 da 939.
Yanzu dai Gwamnan Abba Kabir na da damar daukaka kara a Kotun Daukaka kara zuwa Kotun Koli don neman kotunan su warware wancan hukunci na kotun zaben.
Gwamnan ya fadi a wani taron manema labarai cewa “Mun umarci lauyoyinmu su gaggauta daukaka kara domin dawo da hakkin al’umma.
“Abu ne da yake a fili mu muka lashe zaben da aka yi a watan Maris da kuri’u mafiya yawa, amma bangaren hamayya suka je kotu suka kalubalanci wannan nasara ta al’ummar Kano.”
A gefe guda kuma masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum na ganin cewa idan har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu kwararun lauyoyi tare da gamsassun hujjoji zai iya gamsar da kotunan sama nasara ta dawo gare shi kamar yadda lauyan nan mai fafutikar kare hakkin dan Adam a Jihar Kano Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana.
“Duk da yake cewar shari’a kamar mace ce da ciki, ba a san abin da za ta haifa ba, amma ana ganin cewa matukar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya iya gamsar da kotunan gaba da hujjoji ta hanyar yin amfani da kwararrun lauyoyi, to, babu shakka nasara za ta iya dawowa gare shi kai- tsaye, ko kuma hukuncin ya ba shi dama ya sake samun nasara idan aka samu hukuncin a sake yin zabe a wasu mazabun da ke jihar.”
Ana ganin cewa wannan hukunci zai iya zama izina ga gwamnatin ta Kano wajen yi mata kaimi wajen gudanar da ayyukan da suke gabanta kamar yadda Gwamnan a jawabinsa na bayan yanke hukuncin ya nuna.
Ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke ba zai kashe masa gwiwa ba wajen ci gaba da yi wa al’umma aiki.
Ga dukkan alamu za a iya cewa Gwamnan da gaske yake domin zuwa yanzu ya ci gaba da ayyuka a jihar inda ake shirye shiryen fitar da ’ya’yan jihar don karo karatu a kaasashen waje.
Haka kuma a kwanan nan gwamnatin ta Abba ta dauki nauyin tura wata yarinya mai suna Nana Muhammad don neman maganin ciwon ido a kasar Indiya.
Haka kuma a ranar Litinin gwamnatin ta gabatar da kwarya-kwaryar kasafin kudi ga Majalisar Dokokin Jihar.
Haka a yanzu haka gwamnatin na ci gaba da shirye- shiryen gudanar da auren zawarawa a jihar wanda ake sa rai za a yi shi nan da mako biyu masu zuwa.
Adawa tsakanin Kwankwaso da Ganduje
Tun bayan da dangantaka ta yi tsami a tsakanin madugun Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamnan Jihar Knao Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Mataimakinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda shi ne Shugaban Jam’’iyyar APC na Kasa a yanzu, kan ’yan siyasar jihar ya rabu biyu.
Wannan ya haifar da tumbatsar tsofaffin gwamnonin wadanda ke hamayya da juna inda kowane a cikinsu yake ganin wuyansa ya yi kauri kuma karansa ya kai tsaiko, don haka ba zai sauko da kan kujearar na kin da ya hau ba wajen sulhuntawa tare da kawar da kiyayya a tsakaninsu a lokutan da wasu manyan mutane suka yi kokarin sulhunta su.
Irin wannan tumbatsar da suka yi ce ta sa suke ja da juna a siyasance inda suka yi karfi tare da kakkafa yaransu a madafun iko.
Idan aka duba a shekarar 2019 Madugun Kwankwasiyya ya nuna wa Ganduje yatsa inda ya hana shi sakat a kokarinsa na neman mulkin jihar zagaye na biyu, ta hanyar tsayar da abokin takararsa a Jam’iyyar PDP a lokacin, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
A wancan lokaci, da kyar Ganduje ya tsallake tarkon da madugun ya dana masa, bayan da aka zargi Mataimakinsa na lokacin da hadin gwiwar Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sule Garo suka je wajen tattara sakamakon zabe, aka zarge su da yaga takardar sakamakon zaben Karamar Hukumar Nasarawa lamarin da ya sa Hukumar INEC, ta sake zabe a karamar hukuma da wasu mazabu lamarin inda a karshe Ganduje ya samu nasara ya koma kan gadon mulkin jihar a zagaye na biyu.
Su Kwankwaso sun shigar da kara a kotun zabe ba su yi nasara ba, haka lokacin da suka daukaka kara a kotunan gaba ba su samu nasara ba.
Haka aka ci gaba da gudanar da siyasa mai zafi a tsakanin bangarorin biyu har aka sake dawowa kakar zabe ta shekarar 2023 inda aka sake gwabza takara a tsakanin banagrorin biyu.
Madugun Kwankwasiyyar ya sake tsayar da Abba Kabir Yusuf a karo na biyu, Ganduje ya tsayar da Mataimakinsa Gawuna a karshe Hukumar INEC ta sanar da Abba a matsayin wanda ya lashe zabe, kafin Kotun Sauraren Kararrkin Zaben ta soke nasarar tasa tare da damka ta ga abokin hamayyarsa tsohon Mataimakin Ganduje.
Baya ga wannan kuma mabiya Kwankwasiyya sun kwashe mafi rinjayen kujeru a Majalisar Dokoki ta Kasa inda suka samu kujerun sanata biyu da na Majalisar Wakilai 18 duk da akwai wadanda ake shari’a a kansu a kotu.
Haka kuma sun lashe mafi yawan kujerun Majalisar Dokokin Jihar.
Zuwa yanzu dai za a iya cewa rigimar siyasa a tsakanin manyan giwayen siyasar biyu ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.