Hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi ya rage mana nauyi — Gwamnoni

Mutane ba su san yadda jihohi ke kashe maƙudan kuɗi wajen ɗaukar ɗawainiyar ƙananan hukumomi ba.

Hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin ƙananan hukumomi ya rage mana nauyi — Gwamnoni

Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya ta ce tana maraba da hukuncin Kotun Ƙoli da ya tabbatar wa ƙananan hukumomi ’yanci.

A jiya Alhamis ne dai Kotun Ƙolin Nijeriya ta haramta wa gwamnoni riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu da ake ware musu daga asusun Gwamnatin Tarayya.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman ya ce ƙungiyarsu za ta yi biyayya ga hukuncin kotun.

Ya bayyana cewa tuni Atoni Janar na kowacce jiha ya buƙaci kwafin hukuncin kotun wanda za su yi nazari a kai yayin da kuma a makon gobe za su yi taro dangane da hukuncin da kotun ta yanke.

Ya ƙara da cewa gwamnonin na murna da karkasa iko dangane da ’yancin ƙananan hukumomin.

“Hakan zai rage wa gwamnoni nauyi, saboda mutane ba su san yadda jihohi ke kashe maƙudan kuɗi wajen ɗaukar ɗawainiyar ƙananan hukumomi ba,” inji shi.

Gwamnan na Kwara ya ce matakin karɓe ikon ƙananan hukumomin daga hannun gwamnoni ba zai shafi jihohin ba, musamman jiharsa ta Kwara da ya ce dama ƙananan hukumomi na da ’yanci, saboda dama a cewarsa ba ɓarnatar da kuɗin ƙananan hukumomin gwamnonin ke yi ba.

“Don haka yanzu sai ƙananan hukumomin su ci gaba da riƙe kansu, musamman a wannan lokaci da ake dab da tabbatar da mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

“Su tabbatar suna biyan albashin ma’aikata sannan sarakunan gargajiya su sami kashi 5 cikin 100 na kuɗin da ake bai wa ƙaramar hukumar, waɗannan su ne manyan batutuwan.”

Wani ɓangare na hukuncin shi ne haramta wa jihohin rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin, lamarin da shugaban ƙungiyar gwamnonin ya ce zai shafi wasu gwamnonin, musamman waɗanda ba su da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin a yanzu.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnoni wanda yake tare da takwaransa na Jihar Imo, Hope Uzodinma da kuma na Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce sun gana da Shugaban Ƙasar ne domin tattaunawa wasu batutuwa da suka shafi ƙasa cikin har da mas’alar mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC