Hukuncin Kotun Ƙoli kan zaben gwamnoni ya ɗaga martabar dimokuraɗiyya — Atiku

Atiku ya miƙa sakon taya murna ga gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Hukuncin Kotun Ƙoli kan zaben gwamnoni ya ɗaga martabar dimokuraɗiyya — Atiku

Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya taya gwamnonin jihohin da suka samu nasara a Kotun Ƙolin, yana mai cewa hakan ya ɗaga martabar dimokuraɗiyya a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Debo Ologunagba ya fitar, Atiku Abubakar ya ce hukuncin kotun ƙolin ya tabbatar da nasarar al’ummar jihohin Bauchi da Filato da Akwa Ibom da Zamfara.

Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a Zaben 2023, ya kuma miƙa sakon taya murna ga gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP kan nasarar da ya samu a kotun ƙolin.

“Wannan hukunci ya ba ni damar tabbatar da ƙudurina na cewa haɗin kan jam’iyyun adawa zai taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya Najeriya,” in ji Atiku.

‘“Don haka a shirye nake na jagoranci wannan ɓangare, ta hanyar yin aiki tare da shugabanni da gwamnoni don tabbatar da ci gaban ƙasarmu”.

Haka kuma, a cikin sakon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Wazirin Adamawan ya ci gaba da cewa hukuncin kotun ƙolin ya tabbatar da ƙarfin da jam’iyyarsa ta PDP ke da shi a jihohin da take mulki.

“Ina kira da gwamna Bala Muhammadu na Bauchi da Dauda Lawal na Zamfara da Barista Caleb Muftwang na Filato da Fasto Umo Eno na Akwa Ibom da su ɗauki nasarar da suka samu a kotun ƙolin a matsayin wata dama da za su sake inganta jagorancin da suka riga suka fara kafawa a jihohinsu,” in tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Ya kuma ce “ina da yaƙinin cewa jam’iyyarmu ta PDP za ta ci gaba da kasancewa babbar jam’iyyar adawa a ƙasar, da taimakon gwamnoni da kuma ni kaina, a yayin da za mu tunkari kakar zaɓe mai zuwa.”