Hukuncin Rataya: Ranar Alhamis za a ci gaba da Shari’ar Abduljabbar
An dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Mayun 2024.
Lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, malamin da aka yanke wa hukuncin rataya kan laifin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wassalam, ya nemi Gwamnatin Kano ta biya shi diyya.
Lauya mai suna Barista Yusuf Sadik, ya bukaci diyyar Naira miliyan 20 ne a gaban Kotun Daukaka Kara ta Jihar Kano a ranar Litinin, lokacin da ta fara sauraron shari’ar da Abduljabbar ya daukaka na kalubalantar hukuncin kisa da aka yanke masa.
Hakan ta faru ne bayan Barista Yusuf ya shaida wa kotun cewa a shirye suke a ci gaba da sauraren shari’ar, amma a lauyan gwamnatin Kano, Barista Bashir Saleh, ya roki kotun ta kara musu lokaci, kasacewar a yanzu ba su shirya ba.
A kan haka ne lauyan Abduljabbar ya nuna rashin jin dadinsa, inda ya ce tun a watan Fabarairun 2024 ya sada lauyan gwamnatin da takardun martaninsu.
- An rufe makarantu saboda cutar kyanda a Adamawa
- Sun yi wa wata tsirara suka yada bidiyon a soshial midiya
Saboda haka ya nemi gwamnatin Kano ta biya shi diyyar Naira miliyan 20 saboda bata masa lokaci da aka yi.
Alkalan kotun, Mai Shari’ar Nasiru Saminu da Mai Shari’a A’isha Mahmud, sun bincika takardun da lauyan Abduljabbar ya yi ikirarin ya sadar da lauyan gwamnatin Kano, inda aka gano cewa a watan Maris ya ba da takaddun martanin ba a watan Fabrairu ba.
Daga bisani ya janye bukatar neman gwamnatin ta biya shi Naira miliyan 20.
A karshen zaman alkalan kotun daukaka karar sun dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 9 ga watan Mayun 2024.