Hukuncin Zaben Kano: Masu shirin zanga-zanga su shiga taitayinsu —’Yan sanda

’Yan Sanda sun ce ba za su raga wa masu shirin zanga-zanga kan hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnan Kano ba

Hukuncin Zaben Kano: Masu shirin zanga-zanga su shiga taitayinsu —’Yan sanda

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Hussaini Muhammad Gume,

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ba za ta raga wa masu neman tayar da tarzoma a jihar kan hukuncin kotun da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamnan jihar ba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya gargadi masu neman shirya zanga-zanga ko tatttakin a jihar kan hukuncin kotun da cewa duk wanda runduna ta samu yana karya doka a jihar, zai yaba wa aya zaki.

Kakakin rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ya ce gargadin yana da muhimmanci saboda rahotannin da suka samu kan yadda magoya bayan wata jami’iyya ke amfani da wasu hanyoyiyn bayan fage wajen kiran jama’a da su fito kan titunan Kano domin zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka karar.

A ranar Juma’a 17 ga wata ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta kara kwace kujerar Gwamnan  Kano daga hannun Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, bisa hujjar rashin kasancewarsa dan jam’iyyar kafin zaben da ya kai shi kan kujerar.

Hukuncin kotun da Abba ya daukaka  kara zuwa gare ta ya jawo ce-ce-kuce, kamar wanda kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar, wadda ta fara kwace kujerar Abba, a watan Satumba, ta ba wa babban abokin hamayyarsa, Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC.

Game da shirin zanga-zangar, Kiyawa ya ce, “Mun samu rahoton shirin masu zanga-zangar na tsayar da harkoki da ma tayar da hankali a Kano, shi ya sa muke gargadin jama’a da su yi hattara; Duk wanda zai yi zanga-zanga to ya wajibi ne ya yi a bisa yadda doka ta tsara.

“Sannan a sani cewa ranar Alhamsi, 16 ga Nuwamba, 2023, jajibirin zaman kotun daukaka karar, rundunarmu ta yi zama da shugabannin jam’iyyun NNPP da APC inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya,” a Kano, duk yadda hukuncin kotun ya kasance.

“Sun amince a hana kowane irin taron siyasa, sannan magoya bayansu ba za su yi kowane irin abu mai alaka da zanga-zanga ko tattaki ko biki ko lafazi da zai iya tunzura jama’a ko jawo martani ko wata matsalar tsaro ko cin mutuncin bangaren shari’a ba.”

Don haka kwamishinan ya shawarci Kanawa da su kwantar da hankalinsu, amma su guji duk wani haramtaccen tattaki ko zanga-zanga ko tashin hankali da aka kira su.