‘Hukunta duk wanda ya yi wa PDP zagon ƙasa ya zama dole’

Jam’iyyar PDP ta ce ta fara ɗaukar matakar ɗinke ɓarakar da ta kunno kai a tsakanin ’ya’yanta. Jam’iyyar dai ta ce tuni ta ɗauki matakin ladabtar da ’ya’yanta da ta ke zargin su da yi mata zagon ƙasa da ya sa wasu ke mata kallon kyanwar Lami a fagen siyasa. Rikicin baya-bayan nan da ya […]

‘Hukunta duk wanda ya yi wa PDP zagon ƙasa ya zama dole’

Tambarin PDP

Jam’iyyar PDP ta ce ta fara ɗaukar matakar ɗinke ɓarakar da ta kunno kai a tsakanin ’ya’yanta.

Jam’iyyar dai ta ce tuni ta ɗauki matakin ladabtar da ’ya’yanta da ta ke zargin su da yi mata zagon ƙasa da ya sa wasu ke mata kallon kyanwar Lami a fagen siyasa.

Rikicin baya-bayan nan da ya shafi Jam’iyyar ta PDP, ya sa wasu daga cikin jiga-jiganta mayar da hanakali wajen sasanta ɓangaren shugaban jam’iyyar Ambasada Umar Damagun da wasu ƙusohin jam’iyyar.

Wannan takun sakar dai, ya sa jam’iyyar ta rabu gida biyu, inda ɓangren da ke goyan bayan shugaban jam’iyyar, Umar Damagun ya dakatar da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar da mai ba ta shawara kan harkokin shari’a, yayin da shi kuma ɗaya ɓangaren ya dakatar da Umar Damagun daga muƙaminsa na shugaban riƙo, inda suka maye gurbinsa da Alhaji Yayari Muhammad.

Bala Muhammad shi ne Gwamna Jihar Bauchi kuma Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar PDP ya ce, suna nan kan bakarsu ta kowa ya tsaya a inda yake, za su duba yadda dokar jam’iyyar ta ce don ganin an sami daidaito a tsakanin ’yan jam’iyyar.

A cewarsa, ”Za mu yi ƙoƙari waje ganin an sami haɗin-kai a tsakanin ’yan jam’iyyarmu, musamman ganin yadda har yanzu al’ummar Nijeriya na ra’ayin Jam’iyyar PDP, wadda kuma ita ce za ta kawo masalaha a Nijeriya, tunda muna da ƙwararu da masana makamar aiki da za su fitar da ƙasar daga halin da take ciki.

Haka kuma ya ce, an kafa kwamiti ƙarƙashin Cif Tom Otimi, wanda za su ladabtar da ko waye ko wane ne ko wanda ya yi izgilanci ko ya yi rashin kunya ko tunƙaho da ya kai ga cin mutuncin jam’iyyar ko zarafin ɗan jam’iyya, komai girmansa kuma ko waye shi ko da kuwa ni ne,” inji Bala Muhammad.

Haka kuma ya ce, a halin da ake ciki yanzu, sun ɗinke dukkan wata ɓaraka da jam’iyyar take fuskanta saboda irin matakan da suka ɗauka.