Hushpuppi: Abba Kyari zai san makomarsa ranar 29 ga Agusta
Mai Shari’a Inyang Ekwo ya tsayar da ranar ne bayan lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da bayanai sun kuma amince da hujjojinsu kan lamarin.
DCP Abba Kyari
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan bukatar tura DCP Abba Kyari kasar Amurko domin amsa tambayoyi kan Badakalar Hushpuppi.
Kotun ta sa ranar ce domin yanke hukunci kan karar da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) ya shigar kan DCP Abba Kyari da aka dakatar, bisa zargin sa da alaka da Ramon Abbas (Hushpuppi) wanda ake zargi da damfara ta intanet a kasar Amurka.
- Buhari bai ce gwamnoni su zabo dan takarar shugaban kasa ba —Femi Adesina
- Jiragen yaki ba za su iya kawar da ’yan bindiga ba —Farfesa Usman
Mai Shari’a Inyang Ekwo ya tsayar da ranar ne bayan lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da bayanai sun kuma amince da hujjojinsu kan lamarin.
Gwamnatin tarayya ta nemi a mika Kyari ga kasar Amurka domin amsa wata shari’a da ake zargin shi da alaka da Hushpuppi.
DCP Abba Kyari shi ne tsohon shugaban sashen ’yan sanda sa IRT masu yaki da masu garkuwa da mutane.
An shigar da karar ne a karkashin dokar kasa da kasa, a zaman wani bangare na amincewar gwamnatin Najeriya na bukatar Amurka ta mika mata Kyari.
S halin yanzu Kyari da wasu mutane shida suna fuskantar shari’a ta daban kan zargin safarar miyagun kwayoyi a gaban wata kotun, karkashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite.