Husuma don kare karya yanki ne na munafunci (2)

Daga Hudubar Sheikh Abu Ibrahim Sa’ud Ibnu Ibrahim as-ShuraimMasallacin Haramin Ka’aba da ke Makka Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (RH) ya ce, “Idan ka nazarci abin da ke faruwa a wannan al’umma na sabani a tsakanin malamanta da masu ibadarta da shugabanninta da jagororinta, za ka iske mafi yawansa irin wannan ne, wato shi ne yin […]

Husuma don kare karya yanki ne na munafunci (2)
Husuma don kare karya yanki ne na munafunci (2)

 Sheikh Abu Ibrahim Sa’ud Ibnu Ibrahim as-ShuraimDaga Hudubar Sheikh Abu Ibrahim Sa’ud Ibnu Ibrahim as-Shuraim
Masallacin Haramin Ka’aba da ke Makka

Shaihul Islam Ibnu Taimiyya (RH) ya ce, “Idan ka nazarci abin da ke faruwa a wannan al’umma na sabani a tsakanin malamanta da masu ibadarta da shugabanninta da jagororinta, za ka iske mafi yawansa irin wannan ne, wato shi ne yin zalunci ta hanyar tawili ko ba ta tawili ba, alhali asalin al’amari shi ne jinin Musulmi da dukiyarsu da mutuncinsu haramtacce ne a tsakaninsu, ba su halatta sai da izini daga Allah da ManzonSa (SAW).”
Don haka ya bayin Allah! Mai fajirci a wajen husuma ba ya da iyaka ko wani abu da ke tsare shi a cikinta. Iyaka ya kai ga burinsa, kuma wannan fajirci a cikin husuma ya shafi hakkoki ne ko kudurce-kudurce ko dabi’u.
Duk wanda ya lura da halin da Musulmi suke ciki a yau, da abin da ake ji daga kafofin watsa labarai na karantawa ko kallo ko saurare, zai samu nau’o’in wadannan abubuwa, wato za a ga wayewar dalibin ilimi ko dan jarida, ita ce a yi ta ja-in ja ana husuma domin cimma wata biyan bukata da bankado abin da yake boye, a karshe sai ya zamo abin da ake cimmawa, shi ne idon yarda da take boye mummunan abu, ko idon adawa mai munanta abin da yake mai kyau.
“Ya ku wadanda suka yi imani! Kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane, mai yiwuwa ne (wadanda ake yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata, mai yiwuwa ne su kasance mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, wadannan su ne azzalumai.” (k: 49: 11).
Allah Ya yi mana rahama ni da ku cikin Alkur’ani Mai girma. Kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na daga ayoyi da ambato mai hikima. Na fadi abin da na fada, in ya dace daga Allah ne, idan kuma ya zama kuskure, to daga gare ni da kuma Shaidan, kuma ina neman gafarar Allah, lallai Shi Mai yawan gafara ne Mai yawan jin kai ne.
Huduba ta Biyu
Godiya ta tabata ga Allah Shi kadai, Tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa Annabin da ba wani a bayansa.
Bayan haka, ku bi Allah da takawa ya ku bayin Allah! Ku sani mutumin da Allah Ya fi ki shi ne mai tsananin husuma kan karya da kauce wa gaskiya, kamar yadda ya inganta daga Annabi (SAW) a cikin Sahihaini da waninsu. Kuma Allah Ya bayar da misali kan haka cikin fadinSa: “Sa’annan abin sani kawai, Mun saukakar da shi (Alkur’ani) a harshenka, domin ka yi bushara da shi ga masu aiki da takawa, kuma ka yi gargadi da shi ga mutane masu tsananin husuma. (Ma’ana masu yin jidali don kare karya, masu karkace wa gaskiya a cikin jidali da husuma)” (k: 19: 97).
Wani daga cikin magabata ya ce mafi yawan husumomin da ake yi kan karya ake yin su, don haka ne, Umar bn Abdul’aziz (Allah Ya lullube shi da rahama) ya ce: “Duk wanda ya bijiro wa addininsa da yawan husuma zai rika saurin ciruwa.” Ma’ana ba zai tsaya kan manhaja ayyananniya ba, ko abin da yake a fili ba.
Hafiz Ibn Rajab kuma ya ce: “Idan mutum ya zamo mai tsananin iya husuma ya alla husuma cikin addini ce ko al’amarin duniya har yana iya taimakon karya a kan gaskiya, ya nuna wa mai saurare cewa hakan ne gaskiya, ya wulakanta gaskiya ya mayar da ita surar karya, to wannan yana daga cikin mafiya munin haramatattun abubuwa, kuma mafi kazantar siffar munafunci.”
Ya zo a cikin Sunnan Abu Dawud daga Ibn Umar (Allah Ya yarda da su) cewa Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya yi husuma don kare karya alhali ya san karya ce, ba zai gushe a cikin fushin Allah ba, har sai ya ciru daga haka.”
Ya bayin Allah! Don haka ne ake cewa mai hankali ba shi ne wanda zai iya bambance tsakanin alheri da sharri ba a lokacin husuma, domin mutane da yawa suna iya bambance hakan, a’a mai hankali na hakika, shi ne wanda zai iya mayyaze mafi alherin alhairai da mafi sharrin sharrori. Babu abin da ke jefa masu fadawa cikin husuma ta addini ko harkar duniya ko akida ko wata fikira ko wayewa ko ilimi, sai saboda jahiltar wannan al’amari mai girma. Hakika ya kyautata magana wanda ya rera baitin nan da ke cewa:
Lallai mai hankali shi ne wanda idan cuta biyu suka bayyana a jikinsa, yakan fara warkar da mafi hadari.
A cikin tarihi za mu iske misalai da dama na adalci dangane da husuma da sabani, kuma za mu bayar da misalai guda biyu kacal kan sabanin aiki da akida:
A game da sabani a aiki, za mu ga wani mai sharhi kan Sahihul Buhari yana ta’aliki a kan mas’alar da Buhari ya yi ittifaki da ra’ayin Hanafiyya sai ya ce, “Buhari ya yi ittafaki da Hanafiyya a wannan mas’alar duk da yawan sabawarsa gare su, sai dai kuma dalili ne ya sa shi yin haka.”
Misalin sabani a kudurce-kudurce shi ne: matsayin Shaihul Islam Ibn Taimiyya (Allah Ya yi masa rahama) da Razi, wanda ya auka ga bata a game da akida da manhaja abar ki, sai Shaihul Islam ya kebance shi da rubutun da ya kai mujalladai masu yawa don mayar masa da martani. Amma duk da haka game da shi, Shaihul Islam din ya ce: “Daga cikin mutane akwai mai mummunan zato game da shi –wato Razi- kan cewa yana yin karya da gangan, wannan ba haka ba ne, yakan yi magana ne da abin da yake da shi na ilimi da bincike da nazari a kowane mukami cikin abin da ya bayyana gare shi.”
La ilaha illallah! Me ya kai irin wannan adalci ga wanda kuke husuma da sabani da shi? Wane irin rashin zalunci da fajirci ne wannan ga abokin husuma?
Da wannan sai ku yi salati- Allah Ya yi muku rahama- a bisa mafificin halitta, kuma mafi tsarkin bani Adam.

Sanarwa

Wannan fili yana maraba da hudubobi daga masallatan da ke sassan kasar nan. Ana iya aiko hudubobin cikin Larabci ko Turanci ko Hausa ta adireshinmu Imel dinmu: [email protected] ko ta P.O Bod 6873, Wuse, Abuja