Hutu ko aiki?
Wani dan sanda ne yana gadi a wani wuri, sai ga wani matashi ya zo wucewa, sai ya ce masa: “Oga, barka da hutawa!” Da dan sanda ya ji haka, har matashin ya kusa wucewa, sai ya kira shi. Da ya zo sai ya ce masa ya zauna. Shi kuwa ya samu wuri ya zauna, […]
Wani dan sanda ne yana gadi a wani wuri, sai ga wani matashi ya zo wucewa, sai ya ce masa: “Oga, barka da hutawa!” Da dan sanda ya ji haka, har matashin ya kusa wucewa, sai ya kira shi. Da ya zo sai ya ce masa ya zauna. Shi kuwa ya samu wuri ya zauna, dan sanda ya bar shi tsawon lokaci bai ce masa komai ba. Can da ya gaji sai ya ce masa: “Yallabai, ka ce in zauna, amma ba ka ce mani komai ba.” Shi kuwa sai ya amsa da cewa: “Ba cewa ka yi hutawa nake ba? Kai ma sai ka huta!”
Daga Hajiya A’ishatu Abdullahi