Ibadar Aure dauke da juna-biyu (2)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen amsoshin tambayoyi da suka danganci ibadar aure lokacin goyon ciki. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, kuma ya amfanar […]

Ibadar Aure dauke da juna-biyu (2)
Ibadar Aure dauke da juna-biyu (2)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga karashen amsoshin tambayoyi da suka danganci ibadar aure lokacin goyon ciki. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.
Tambaya ta 6: Ko akwai wasu lokuta da ya kamata ma’aurata su kiyaye wajen yin ibadar aure yayin goyon ciki? Kuma wadanne matsaloli ne in suna tare da mai juna biyu ya kamata a guji yin ibadar aure.
Maman Sudays, Funtua.
Amsa: Babu wani kayyadajjen lokacin da ma’aurata za su kiyaye gabatar da ibadar aure matukar sun tabbatar juna biyun nan lafiyayye ne, kuma ba ya tattare da kowace irin matsala, za su iya gabatar da ibadar aure koda kuwa lokacin haihuwa ya karato sosai, matukar babu wata takurawa ga uwargida. Amma idan ya kasance uwargida ta taba yin bari, ko haihuwar bakwaini, to ya fi alfanu ma’aurata su daure, su guji gabatar da ibadar aure har sai ta sauke. Haka idan ya kasance jini na zuba daga ‘yanmatancin uwargida, ko ruwan faya yana yawan digowa, ko in uwa ta rufe kofar mahaifa, ko in kofar mahaifar ya fara budewa tun kafin lokaci ya cika da sauran matsaloli makamantan hakan.
Tambaya ta 7: Tun da na samu ciki sai na ji ba na son maigida ya kusance ni ko kadan, kuma sai in rika jin ba na son ganinsa, shin mene ne ke haifar min da haka?
-Baiwar Allah
Amsa: Wannan daya ne daga cikin ire-iren ilimbo da tsirowar ciki ke haifarwa ga mafi yawan masu juna biyu. Sha’awa na daukewa gaba daya ga mafi yawan mata lokacin da suke dauke da juna biyu; wasu a farkonsa, wasu a tsakiya wasu kuma sai cikin ya tsufa. Duk mai cikin da ta ji cewa sha’awarta ta dauke mata, ta sani wannan ba wani abin damuwa ba ne, kuma matsala ce ta wucin gadi, daga sauke nauyinta ko ma kafin ta sauke shi sha’awarta za ta dawo. Magidanta maza kuma sai su yi hakuri da juriya, su fahimci cewa wannan wani yanayi ne na masu ciki, kada su rika jin haushinsu ko su kullace su, domin ba su suka dora wa kansu wannan matsalar ba, yanayin cikin ne ya zo da haka, dole su taimaka masu har su sauke lafiya ta dukkan hanyoyin da suka dace. Musamman idan aka yi la’akari da yadda irin wannan takurawar ke iya zama sanadiyyar daskarar da sha’awar wasu matan, ta yadda ko bayan sun haihu sha’awarsu ba za ta dawo daidai kamar da ba. Don haka idan har mace ta ji ba ta da sha’awar ibadar aure a dalilin shigar ciki, sai ta tattauna da maigida don cim ma abin da suka ga ya fi dace musu, domin ba dole sai an yi ainihin ibadar aure ba ne za a iya samun aminci daga motsuwar sha’awa.
Tambaya ta 8: Tun da amarya ta samu ciki sai na ji kwata-kwata sha’awata ta dauke gaba daya, ita kuma sai tata sha’awar ta karu sama da kafin ta samu cikin. Don Allah ya zan yi sha’awata ta dawo daidai kamar da?
Bawan Allah.
Amsa: Wasu magidanta kan fuskanci matsalar rashin sha’awar matansu lokacin da suke dauke da juna biyu; wannan na faruwa ne saboda dimbin canje-canje da juna biyu ke kawowa ga mafi yawan mata, irin su zubar da yawu, yawan amai, yawan laulayi, saurin gajiya, digar ruwan nono, da sauransu. Wasu kuma a lokacin ne sha’awar da suke wa matansu ke kara hauhawa musamman idan alamar cikin ta fara bayyana a jikin matan nasu. Kowace mace tana son a ce mijinta yana sha’awarta kodayaushe, hakan na matukar kwantar mata da hankali, bayyanar da rashin sha’awarta gare ta kuma na iya darsa mata kuncin zuciya; don haka duk da cewa sha’awarka ta dauke dole ka yi kokari ka boye hakan daga gare ta, kuma ka kara kaimi don nuna kulawarka gare ta don kyautata zamantakewa, domin idan ta fahimci ba ka sha’awarta a dalilin juna biyunta, wannan zai kara nauyayar mata da zuciya.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.