IBB ya gargadi ’yan Najeriya kan zubar da jini
Tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya bukaci ’yan Najeriya su guji furta kalaman kiyayya da sauran take-taken da ka iya tayar da tarzoma da zubar da jini a kasar. A sanarwar da ya fitar don tunawa da mazan jiya na shekarar 2018, tsohon shugaban mulkin sojan ya ce kasar Najeriya tafuskanci tashe-tashen […]
Tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya bukaci ’yan Najeriya su guji furta kalaman kiyayya da sauran take-taken da ka iya tayar da tarzoma da zubar da jini a kasar.
A sanarwar da ya fitar don tunawa da mazan jiya na shekarar 2018, tsohon shugaban mulkin sojan ya ce kasar Najeriya tafuskanci tashe-tashen hankula da suka janyo zubar da jini saboda haka sai ya yi kira da a dauki matakan gaggawa don kawo karshen lamarin.
“A matsayinmu na mutane ya zama wajibi mu cusa soyayyar kaunar al’adunmu da suke koyar da zaman lafiya da juna. Ya zama wajibi mu guji kalaman batanci da kiyayya da sauran abubuwan da ka iya tayar da tarzoma”. Inji shi.