Ibe ya zabi Ingila a kan Najeriya

dan Najeriya da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da ke Ingila, mai suna Jordan Ibe ya tabbar da cewa ya fi sha’awar buga wa Ingila kwallo maimakon Najeriya.Ibe mai shekara 19, yana da zabin kasar da zai wakilta tsakanin Ingila da Najeriya, bayan da ya buga wa tawagar matasan Ingila ’yan […]

Ibe ya zabi Ingila a kan Najeriya
Ibe ya zabi Ingila a kan Najeriya

dan Najeriya da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da ke Ingila, mai suna Jordan Ibe ya tabbar da cewa ya fi sha’awar buga wa Ingila kwallo maimakon Najeriya.
Ibe mai shekara 19, yana da zabin kasar da zai wakilta tsakanin Ingila da Najeriya, bayan da ya buga wa tawagar matasan Ingila ’yan shekara 21 wasanni biyu a watan Satumba.
Sunday Oliseh ya yi niyyar gayyato Ibe cikin tawagar ’yan wasan Najeriya domin ya buga mata wasa, amma sai iyayen dan wasan suka kira kocin na Najeriya suka shaida masa cewa Ibe ya zabi ya taka wa Ingila leda.
Ibe wanda aka haifa a Landan ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta matasa ’yan shekara 21 ta kasar Ingila a wasannin da ta yi da Amurka da Norway.