Ibo ba su da godiya, ’yan Neja-Delta kuma mabarnata ne – Joe Igbokwe

Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC reshen Jihar Legas Mista Joe Igbokwe, ya bayyana cewa ’yan kabilar Ibo ba su da godiyar Allah yayin day a bayyana kabilun yankin Neja-Delta da mabarnata.Mista Joe Igbokwe ya fadi a wani rubutu da ya aike wa gidajen jaridu da dama a wannan mako cewa tun lokacin da Shugaban […]

Ibo ba su da godiya, ’yan Neja-Delta kuma mabarnata ne – Joe Igbokwe
Ibo ba su da godiya, ’yan Neja-Delta kuma mabarnata ne – Joe Igbokwe

Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC reshen Jihar Legas Mista Joe Igbokwe, ya bayyana cewa ’yan kabilar Ibo ba su da godiyar Allah yayin day a bayyana kabilun yankin Neja-Delta da mabarnata.
Mista Joe Igbokwe ya fadi a wani rubutu da ya aike wa gidajen jaridu da dama a wannan mako cewa tun lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben bara da ya yi ta wahalar nema tun shekarar 2003 da 2007 da 2011 da kuma 2015, dimbin mutane daga yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas suke ta fadi munanan maganganu da kiransa da miyagun sunaye da zagi da bata shi da bata shugabancinsa da kamfe din kiyayya da kawo rarraba ta kabilanci.
“Ina bibiyar irin wannan muguwar dabi’a sama da shekara guda ke nan, kuma an ki sassautawa. Tana dada ruruwa kamar wutar daji a kullum. A baya-bayan nan mutane Kudu maso Kudu wadanda dansu ya fadi a zabe sun fara mika wuya sai wadanda suke yi domin aljifansu wadanda suke lalata muhallinsu. Na fara ganin yunkuri na gaskiya daga shugabannin Kudu maso Kudu don dawo da zaman lafiya a yankin Neja-Delta kuma ina yaba musu kan haka, wannan domi amfani kansu ne,” inji Igbokwe.
Ya ce wannan kasa ta kai yadda take ne a yau saboda sadaukarwa ciki har da na jini, amma ’yan kabilar Ibo marasa godiyar Allah da tsagerun Neja-Delta suke son wargaza kasar saboda son kai.
Mista Igbokwe ya ce, tsagerun Neja-Delta suna lalata bututun mai kuma sun kawo cikas ga samar da wutar lantarki ta hanyar lalata bututun gas. Kuma sun lalata kasar nomad a ruwa a yankunansu tare da kawo illa ga rayuwa. Ya ce baya ga Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC) da Ma’aikatar Neja-Delta da ba su kashi 13 cikin 100 na duk kudin fetur din da aka sayar, Gwamnatin Tarayya ta kuma bullo da shirin afuwa ga tsagerun yankin inda ake biyansu kudin alawus kusan shekara goma yanzu. Sannan lokacin da Jonathan ya mulki kasar nan na shekara shida ya yi amfani da wannan dama ya samar musu da dimbin ayyuka.
 Mista Igbokwe ya ce baya ga mayar da tsagerun Neja-Delta biloniyoyi ba tare da aikin komai ba, an nada mutanen yanki a shugabancin wurare masu maiko. “To me kuma suke bukata? Wadannan ’yan iska da ke zubar da jini da suke kiran kansu Abengers, ba su da wata fatar alheri. Su cikakkun ’yan iska ne kuma mabarnata. Kuma sun yi kadan ba su isa su tilasta wannan gwamnati ta mika musu wuya ta hanyar barazana da zare ido ba,” inji shi.
Ya ce sun yi wa Obasanjo barazana sun yi wa ’Yar’aduwa yanzu suna yi wa Buhari, yanzu sun zo iyaka babu inda za a gusa. “Idan Shugaban kasa zai murkushe Boko Haram, wadannan shashashun Abengers ba su isa yin komai ba,” inji Igbokwe.
Ya zargi shugabannin yankin Neja-Delta da sace danyen man fetur na biliyoyin Dala, bayan Najeriya tana kashe biliyoyin Naira wajen horar da dubban tsagerunsu da yaransu a nan Najeriya da wajenta , inda ya ce lokaci ya yi da za a dakatar da wannan rashin hankali. “A wurina man fetur ba komai ba ne, ya wajaba Najeriya ta koma bangaren aikin gona,” inji shi.
Da ya koma kan masu fafutikar neman kasar Biyafara, Mista Igbokwe ya bayyana hakan da wasan yara don haka mutane su daina kashe kansu haka kawai.
Ya ce “Mutanenmu sun kasa fahimtar duniya ta canja, a waje da nan cikin gida, a makarantu da kasuwanni a kan tituna da coci-coci da tarurrukan garuruwa ’yan kabilar Ibo sun kasa fahimtar duniya ta canja. Duk wani yunkuri da Shugaba Buhari zai yi don sake gina kasar nan sai sun zage shi, sun bata shi sun ba abin ruwan kabilanci. Wannan mummunan abin kunya ne ya sanya tilas in yi magana.” Ya ce yayin da shugabannin yankin Neja-delta suka fara nemo maslaha shugabannin Ibo sun yi gum da bakunansu, kuma hakan ba alheri ba ne. Ya ce kamfe din batunci da kiyayya da Ibo a ciki da wajen kasar nan ke yi ga Shugaba Buhari yana jefa mutanensu da ke zaune a sassan kasar nan ne a cikin hadari.
“Shugaba Buhari ya fito ne daga wani sashi na Najeriya kuma ba yadda za a yi ya ce mutanensa suna jin dadi a lokacin da muke cin mutunci da bata dansu. Babu wata kabila da ta yi kaura zuwa sassan Najeriya irin Ibo. Suna zaune suna kasuwanci a kusan kowane sashi, duk lokacin da muka jefi wani da dutse muna jifa rayuwar danginmu da harkokin kasuwancinsu da ke wadancan sassa ne a cikin hadari,” inji shi.