Ibrahim Abubakar: Dan Ga-ruwan da ya zama lauya

Barista Ibarhim ya ce a kango ya rika kwana a Makarantar Horon Lauyoyi.

Ibrahim Abubakar: Dan Ga-ruwan da ya zama lauya

Barista Ibrahim Abubakar wanda aka fi sani da Mai Kayan Law ya samu nasarar zama cikakken lauya bayan da ya kammala Makarantar Horon Lauyoyi ta Kasa da ke Bwari, Abuja.

A hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya dauki nauyin karatunsa ta hanyar sana’ar ‘Ga-ruwa’ da sauran gwagwarmayar rayuwa da ya sha:

Aminiya: An san cewa kai dan ga-ruwa ne, ga shi kuma yanzu ka zama lauya, yaya hakan ya kasance?

Na fara wannan gwagwarmaya ce tun ina makarantar sakandare lokacin da mahaifina ya rasu.

Mun shiga wani mawuyacin hali na rayuwa ta yadda tilas na je na karbi hayar kurar ruwa daga makwabta na fara ga-ruwa.

Da ’yan kudin da nake samu a sana’ar ce na biya wa kaina kudin makarantar sakandare da kuma karamar difloma a fannin shari’a a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Jihar Bauchi.

Kuma sai da na rubuta jarrabawar shiga jami’a sau uku, kuma na rubuta jarrabawar kammala sakandare wato WAEC da NECO har tsawon shekara takwas a jere wato daga 2001 zuwa 2008 kafin in samu nasarar cin darasin harshen Ingilishi don samun shiga jami’a.

Aminiya: To ta yaya kake samun kudin yin rajistar jarrabawar?

Da yake na sa a zuciyata cewa sai na zama lauya a rayuwata, sai da ta kai ga na sayar da duk wani abu da na mallaka ciki har da wani Alkur’ani Mai girma da na gada daga mahaifina.

Sannan kuma ina da juriya a sana’ata ta ga-ruwa don tsira da mutuncina.

Haka na samu taimako daga wata yayata da sauran ’yan uwa da abokan arziki.

Amma a gaskiya na shiga cikin kunci da wahala sosai kafin in kammala karatun difloma.

Aminiya: Kana nufin har a lokacin da kake karatu a makarantar gaba da sakandare kana yin ga-ruwa?

Kwarai kuwa, domin ina cikin matsi kuma ba ni da wanda zai dauki nauyin karatuna.

Kuma a lokacin zan iya yin ga-ruwa in samu kudi da safe kafin in je aji ko da yamma bayan na dawo.

Aminiya: Ko a lokacin kakan ji kunya ko boye wa abokan karatunka musamman ’yan mata yanayin sana’arka?

A’a, ban taba boye wa kowa sana’ata ba. Kai zan iya tunawa ma akwai wata ’yar ajinmu da idan na kai ruwa gidansu sai ta daure fuska ta kalli wani waje kamar ba ta taba sanina ba.

Sannan idan mun hadu a aji sai ta rika gulmata kai ka ce bara ta ga ina yi.

Aminiya: Ko irin wadannan mutane sun taba karya maka gwiwa?

Sam, babu wanda ya taba sanyaya mini gwiwa. Domin da farko ni ban dauki kaina kowa ba.

Ina dai kokarin ganin na cim ma burina har in zama wanin. Kuma na san hakan ba abu ne mai yiwuwa ta sauki ba.

Na ci karo da mutane masu kyara irinta da dama wadannsu ma ’yan uwa ne da suka yanke kaunar ba zan taba zama lauya ba saboda talaucina.

Haka ko a lokacin da na kammala karatun jami’ata a Jami’ar Bayero na ci karo da mutane da dama da suka yi mini wulakanci saboda kawai na je wurinsu neman taimakon kudin da zan yi rajista zuwa Makarantar Horar da Lauyoyi ta Kasa. Amma dai yanzu duk na yafe musu.

Aminiya: Ko a Jami’ar Bayero ma ga-ruwa kake lokacin da kake karatu?

A’a, lokacin da nake karatu a Bayero takardun karatu nake sayar wa abokan karatuna.

Wannan shi ya sa aka yi mini lakabi da ‘mai kayan law.’ Akwai malamai da dama na Tsangayar Ilimin Shari’a ta Jami’ar Bayero da Allah Ya sa suka fahimci halin da nake ciki.

Su ne suke taimaka mini da takardun karatun da dalibai suke bukata, ni kuma sai in gurza su da yawa in rika sayar wa dalibai ina samun na cin abinci.

Haka kuma a duk lokacin da aka je hutu ba na zuwa ko’ina sai in zauna a makaranta.

Wannan ne ya ba ni damar rika yi wa daliban da suke nesa da Kano rajistar makaranta.

Sukan turo mini da lambarsu ta jami’a da kudin rajistar, sannan su dora Naira dubu biyu ko uku a sama a matsayin dan ihsani gare ni.

Ta haka na samu na kukuta har na kammala karatun jami’ata.

Amma zan iya tunawa gaba dayan shekarata ta farko a jami’ar a masallaci nake kwana kafin daga bisani in koma kwana tare da wadansu abokaina.

Aminiya: To yaya rayuwa ta kasance a Makarantar Horar da Lauyoyi ta Kasa?

A can ma dai an ji jiki sosai. Domin kuwa farkon shekarar da na fara zuwa faduwa na yi a jarrabawar.

Kuma wadansu bayin Allah ne da lokacin ba zai isa in bayyana sunayensu ba suka dauki nauyina.

Wannan zuwa na biyun kuma da na samu nasarar, Mista Samuel Aruwan, Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Kaduna ne ya biya mini kudin makaranta.

A can din ma dai sai da ta kai ina kwana a kango da kuma masallaci.

Aminiya: Da yake yanzu burinka ya cika ka zama lauya yaya kake ji?

Gaskiya ina cike da farin ciki kuma ina godiya ga Allah da Ya ba ni wannan dama.

Kuma ina godiya ga mahaifiyata da ta karfafa mini gwiwa.

Kuma ina godiya ga malamaina da sauran ’yan uwa da abokan arziki da suka taimake ni domin ba don su ba, da watakila abin bai yiwu ba.

Aminiya: To yanzu kuma ina ka dosa?

To gwagwarmaya dai yanzu ma aka fara. Yanzu a kasuwa nake.

Kuma ina kara godiya ga Allah da Ya sa na zama lauya wanda ya kware a fannin Shari’a da Dokoki na bai-daya.

Zan yi iya kokarina in ga na sadaukar da rayuwata wajen tallafa wa mabukata.

Aminiya: Ko kana nufin za ka iya tsaya wa masu karamin karfi wajen kwato masu hakkinsu?

Kwarai kuwa, duba da irin wahalar da na sha a rayuwa idan ban yi haka ba ai ban ma yi wa kaina adalci ba.

Ina tuna a baya lokacin da na ce ina son zama lauya in ba mahaifiyata ba babu wani mutum da ya gaskata hakan.

A Gaskiya na sha wahala da yawa a rayuwata, don haka ne na kuduri niyyar in Allah Ya so sai na kafa gidauniyata wacce zan rika tallafa wa masu karamin karfi.

Aminiya: Wadanne darussa kake ganin matasa za su iya koya daga rayuwarka?

A Gaskiya gaba dayan rayuwata darasi ce ga matasa. Musamman ma ‘ya’yan talakawa.

Ya kamata su sani talauci ba zai iya hana mutum ya zama wani abu ba a rayuwa.

Sannan kuma mafi yawan matasa a yau ragwaye ne masu cike da gani da jin sun isa, ga kuma alfahari.

Wadannan kuwa abubuwa munana da ba za su taba barin mutum ya kai ga gaci ba.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa