Ibrahim Bibi Farouk: Babban bango ya fadi

A ranar Litinin ne tsohon dan siyasa kuma tsohon mukaddashin Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Bibi Farouk ya rasu, mutuwar ta kara haifar da wani babban gibi a fagen siyasar jihar, kasancewarsa wani babban bango abin jingina a harkar siyasa a jihar.Rasuwarsa ta kawo karshen jiga-jigan ’yan jam’iyyar NEPU a karkashin Marigayi Malam Aminu Kano […]

Ibrahim Bibi Farouk: Babban bango ya fadi
Ibrahim Bibi Farouk: Babban bango ya fadi

A ranar Litinin ne tsohon dan siyasa kuma tsohon mukaddashin Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Bibi Farouk ya rasu, mutuwar ta kara haifar da wani babban gibi a fagen siyasar jihar, kasancewarsa wani babban bango abin jingina a harkar siyasa a jihar.
Rasuwarsa ta kawo karshen jiga-jigan ’yan jam’iyyar NEPU a karkashin Marigayi Malam Aminu Kano da suka rage. Misali a makon da ya gabata ne shi ma wani tsohon dan NEPU kuma daya daga dattawan Arewa, Alhaji Magaji Dambatta ya rasu. Haka shekara biyu da ta gabata shi ma wani sanannen dan NEPU kuma daya daga ’yan kishin kasa da suka karbo ’yancin Najeriya, Malam Mudi Spikin ya rasu.
Marigayi Malam Ibrahim Bibi Farouk ya rasu yana da shekara 82 bayan da ya sha gwagwarmaya a fagen siyasar Najeriya, inda har ya rike mukamin mukaddashin gwamnan farar hula na farko a Jihar Kano, wato lokacin Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, wanda shi ma yanzu ya yi kimanin shekara 5 da rasuwa.
Ya rike mukamin mukaddashin gwamnan na kimanin shekara daya. Makusantan marigayi Bibi Farouk sun shaida wa Aminya cewa an tsige shi daga mukamin nasa ne, a sakamakon rikicin siyasar cikin gida da ya haifar da baraka a tsakanin mabiya tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PRP, Malam Aminu Kano da kuma gwamnan Jihar Kano na lokacin da ke karkashin Jam’iyyar PRP. Wannan rikicin ne ya haifar da bangaren ‘Santsi’ na mabiya Gwamna Rimi da kuma bangaren “Tabo” na Malam Aminu Kano.
Alhaji Abdulkarimu dayyabu ya bayyana cewa “Marigayi Bibi Farouk mabiyin Malam Aminu Kano ne, kuma shi ne ya hada shi da Gwamna Abubakar Rimi a matsayinsa na dattijo kuma masanin addini, don ya rika daidaita tafiyar da gwamnati tare da ba da shawara mai amfani ga gwamna.”
Ya ce baya ga ilimin addinin da marigayin yake da shi, mutum ne mai akida da riko da ita da kuma biyayya ga marigayi Malam Aminu Kano. Ya ce kasancewarsa tare da Malam Aminu a bangaren Tabo a lokacin wannan barakar ne ya sa ya rasa mukaminsa.
Ya ce ana zargin jam’iyyar NPN mai mulkin Gwamnatin Tarayya a lokacin ce ta kunna wutar wannan rarrabuwa a cikin jam’iyyar ta PRP, wacce a lokacin ta ke da gwamnoni a jihohin Kano da Kaduna.
Kasancewar marigayi mai saukin kai wanda bai dauki duniya da girma ba, ya sa tun da aka tsige shi daga mukaddashin gwamna sai ya kama harkarsa ta ilimin addini da kuma noma, abin da ya sa har ya koma karkara da zama, ya koma garin Gezawa da ke a gabashin birnin Kano shi da iyalinsa. Daga nan ba a sake jin sa yana maganganu sosai a fagen siyasa ba, duk da cewa shi masanin siyasa ne, saboda kusancinsa da marigayi Malam Aminu Kano.
Ya ci gaba da zamansa a garin Gezawa, daga bisani ya samu rashin lafiya tare da nakasar bangaren jikinsa har na fiye da shekara goma. Bayanai daga dan marigayin, wato Dokta Farouk Bibi Farouk, wanda yanzu mashawarcin gwamnan Kano ne a bangaren hidima da saukar baki, ya ce mahaifin nasu ya rasu ne da kimanin karfe goma sha biyun ranar Litinin, bayan da suka kai shi wani asibiti mai zaman kansa da ke Tarauni, a sakamakon jikinsa da ya tsananta, daga bisani ya rasu. Ubangiji Ya jikan mazan jiya kuma Ya kyautata namu karshen, Amin.