Ibrahimobic ya fara shirin komawa Manchester United
dan kwallon kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Zlatan Ibrahimobic ya fara yunkurin komawa kulob din Manchester United da ke Ingila a karshen kakar wasa ta bana.Rahotannin da ke fitowa daga Faransa sun nuna tuni dan kwallon ya yanke shawarar komawa Ingila don cigaba da kwallo ganin kwantaraginsa a kulob din PSG […]
dan kwallon kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Zlatan Ibrahimobic ya fara yunkurin komawa kulob din Manchester United da ke Ingila a karshen kakar wasa ta bana.
Rahotannin da ke fitowa daga Faransa sun nuna tuni dan kwallon ya yanke shawarar komawa Ingila don cigaba da kwallo ganin kwantaraginsa a kulob din PSG za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana kuma ba shi da niyyar sabunta kwantaraginsa a can.
Wani rahoto da kafar watsa labarai ta Manchester United ta fitar ya nuna yadda dan kwallon ya amince ya koma kulob din don cigaba da kwallo ganin ya iya yaren Ingilishi da hakan ta sa ba zai fuskanci matsala wajen yin hulda ba.
Ibrahimobic, dan kimanin shekara 34 kafin wasan da kulob din ya yi da na Chelsea a ranar Talatar da ta wuce ya yi wa kulob din PSG wasanni 136 kuma ya samu nasarar zura kwallaye 166 a raga ga kulob din tun bayan komarsa kulob din a shekarar 2012.
dan kwallon ya taba yi wa kulob da dama wasa da suka hada da Ajad na Holand da AC Milan da Inter Milan da Jubentus a Italiya da kuma FC Barcelona a Sifen kafin ya koma PSG na Faransa.
Duk da shekarunsa sun yi nisa, wasu daga cikin magoya bayan United suna ganin dan kwallon zai iya taka rawar gani idan ya koma kulob din Manchester United.