Ibrahin Ibrahim: Fim na sauya al’umma cikin sauki
Ibrahim Ibrahim jarumin fina-finan Hausa ne, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya shiga harkar fim, nasarorin da ya cim ma da kuma kalubalen da yake fuskanta a halin yanzu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Tarihina a takaiceAssalamu alaikum sunana Ibrahim Ibrahim wanda aka fi sani da Ibrahim Daddy. An haife ni a shekarar […]
Ibrahim Ibrahim jarumin fina-finan Hausa ne, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya shiga harkar fim, nasarorin da ya cim ma da kuma kalubalen da yake fuskanta a halin yanzu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum sunana Ibrahim Ibrahim wanda aka fi sani da Ibrahim Daddy. An haife ni a shekarar 1989 a Unguwar Rimi da ke Kaduna. Na yi makarantar firamare da sakandare, daga nan na wuce Jami’ar Abuja, inda na kammala digiri a fannin Harkokin Banki da Kudi (Banking and Finance) a shekarar 2008. Na fara harkar fina-finan Hausa ne a shekarar 2006 da wani fim mai suna ‘Sabon Launi’, amma har yanzu fim din bai shiga kasuwa ba saboda wasu dalilai.
Abin da ya ja hankalinka ka fara fim?
A gaskiya sha’awa ce ta sa ni shiga harkar fim. Kodayake hakan bai rasa nasaba da yadda a fahimtata wannan sana’ar take taka muhimmiyar rawa wajen gyara dabi’u da halayen al’umma. Saboda ta hanyar fim ne za ka yi wa jama’a hannunka mai sanda, kuma idan aka yi sa’a, ya sauya halinsa cikin sauki. Dalili da wannan ya sa na ga ya dace ni ma in ba da tawa gudunmuwar ke nan.
Ko yanzu fina-finan da ka yi za su kai nawa?
A gaskiya suna da dama. Kodayake akwai fina-finan da tashar talabijin ta Africa Magic Hausa mai suna ‘dan Baiwa’ da ake sanyawa a ranakun karshen mako. Fim din irin wanda ake kira Series Mobie ne, wanda za ka ga fim ne mai tsawo matuka. Amma a gaskiya ban san yawan fina-finan da na fito a ciki ba.
Wadanne nasarori ka cim ma zuwa yanzu?
Suna da dama. Kodayake, a watan Mayun bana, na samu lambar girmamawa sanadiyyar wani fim da ake kira ‘Auta’ da na fito a matsayin jarumi. Da sauran wasu lambobin girmamawa da dama da na samu a lokuta daban-daban.
Batun kalubale fa?
Alhamdulillahi, rayuwa ba ta rasa kalubale iri-iri. Har ila yau, duk lokacin da kalubale suka bijiro min nakan mayar da komai ga Ubangiji. Amma gaskiya akwai su da dama. Kodayake ba zan iya bayyana su ba, saboda na dauke su ne a matsayin jarrabawa daga Allah. Nakan manta da duka kalubalen, saboda duniya juyi-juyi ce, musamman ma lokacin da na tuna da irin nasarorin da nake ganin na samu a wannan sana’ar.
Burinka a yanzu?
Ba ni da wani abu, saboda abin da nake buri shi ne, in isar da sako . Kodayake, babban burina bai wuce fatan cikawa da imani ba.
Batun Iyali?
Ban yi aure ba.