Ibro bai fi karfin doka ba- Hukumar Tace Fina-finai

A kwanakin baya ne Kotun tafi-da-gidanka da ke karkashin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta haramta wani fim mai suna ‘kara’in Ibro’, sannan ta daure furodusan fim din Ibrahim Bauni shekara daya ko tara da kuma wanda ke dillancin fim Shazali Kamfa shi ma daurin shekara daya ko tara.Kotun ta ki bayyana wa manema […]

Ibro bai fi karfin doka ba- Hukumar Tace Fina-finai

Babban-Daraktan Hukumar Tace Fina-finai Ahmad Dahiru BeliA kwanakin baya ne Kotun tafi-da-gidanka da ke karkashin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta haramta wani fim mai suna ‘kara’in Ibro’, sannan ta daure furodusan fim din Ibrahim Bauni shekara daya ko tara da kuma wanda ke dillancin fim Shazali Kamfa shi ma daurin shekara daya ko tara.
Kotun ta ki bayyana wa manema labarai adadin tarar, sai dai ta ce Bauni ba zai shirya fim na tsawon shekara daya ba, shi ma Shazali ba zai yi dillancin fim na tsawon shekara daya ba.  
Sai dai jita-jita ta watsu a cikin gari cewa Rabilu Musa (Ibro) ya fi karfin doka, kasancewar kotun ta ce bai aikata wani abu na ba daidai ba duk da cewa shi ne jarumin fim din.
Wadansu sun ce ba a hukunta shi ba ne saboda yana daya daga cikin jami’an gudanarwar hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano (board member).
Wakilinmu ya tuntubi Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Ahmed dahiru Beli, kan batun inda ya ce “Ba mu da dan lele a masana’antar shirin fim, duk wanda ya yi ba daidai ba za mu hukunta shi kamar yadda doka ta tanada. Ibro jarumi ne kawai a fim din, ma’ana, duk abin da ya yi, sa shi aka yi. Babban mai laifi shi ne wanda ya shirya fim din.”
Ya ce: A lokacin furodusan ya kawo fim din hukumarsu don a tace shi, hukumar ta ce ya cire wani wuri na badala da kuma tambelen da Ibron ya yi, tare da sauran abubuwan da suka saba wa shari’a a fim din, ya cire su, kamar yadda ya nuna wa hukumar.  Bayan ta ba shi izini sai ya fitar da lalataccen mai cike da kura-kurai kasuwa, saboda da hukumar ta haramta wannan fim din.
Dangane da zargin son kai, Beli ya ce hukumarsu tana aikinta babu sani, babu sabo. Domin a baya ta hukunta Sani Danja wanda yana da mukamai na siyasa a gwammnatin tarayya bayan ya fitar da wani fim da ya saba wa doka.
Idan da za a iya tunawa, hukumar a karkashin Dokta Rabo ta daure Ibro da marigayi Lawal kaura bisa rawar da suka taka a wani fim mai suna ‘Mamar-Mamar.